A karon farko gwamnatin Abba gida-gida ta yi koyi da ta Ganduje

Date:

 

 

A jiya Juma’a ne gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da shirin Lungu Ƙal-ƙal da nufin tsaftace wa da inganta muhalli a unguwannin birnin jihar.

DAILY NIGERIAN ta tuna cewa a lokacin mulkin da, tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ƙaddamar da shirin mai suna Lungu Ƙal-ƙal, inda aka riƙa rufe kwatocin lunguna da feshin maganin sauro a wasu unguwanni a birnin Kano.

FB IMG 1753738820016
Talla

Sai dai shirin ya tsaya kwatsam kuma har gwamnatin ta sauka daga mulki ba a ci gaba ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin da na Facebook, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar Kano, Dr Dahir M Hashim ya ce wannan shiri ne na musamman na Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf domin inganta tsafta, lafiyar muhalli, da tsaro a unguwanni masu cunkoson jama’a.

A cewa Hashim, shirin, wanda aka ƙaddamar da shi a daren juya Juma’a a lokon gidan Ɗan Isa da ke unguwar Yakasai, zai farfado da kyakkyawan yanayin unguwannin Kano ta hanyar gyara hanyoyin ruwa da kuma saka musu fitulu.

Gwamnatin Kano ta amince da kashe Naira biliyan 14 akan ayyukan raya ƙasa

“A daren yau mun ƙaddamar da shirin 𝐋𝐮𝐧𝐠𝐮 𝐊𝐚𝐥-𝐊𝐚𝐥 a lokon gidan Ɗan Isa dake Unguwar Yakasai. Wannan shiri ne na musamman na Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf domin inganta tsafta, lafiyar muhalli, da tsaro a unguwanni masu cunkoson jama’a.

“Ta wannan shiri, zamu farfado da kyakkyawan yanayin unguwannimu ta hanyar gyara hanyoyin ruwa da kuma saka musu fitulu.

IMG 20250802 WA0088(1)
Talla

“Wannan gagarumin mataki na nuna kudirin Mai Girma Gwamna wajen dawo da mutunci ga al’ummominmu da kuma inganta rayuwar kowane mazauni,” in ji Hashim.

Kwamishinan ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa unguwanni sun zama masu tsafta, lafiya, da tsaro ga kowa da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanya mata a shugabanci zai taimaka wajen kawo cigaba ga al’umma – NAWOJ Kano

Kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya (NAWOJ), reshen jihar...

Gwamnan Kano ya raba tallafin kayan sana’o’i ga matasa 1130

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba tallafin...

‎2027: Tsohon SSG Na Kaduna Ya Shawarci Sha’ban Ya Bar APC Ya Shiga ADC Don Yin Takarar Gwamna

Daga Rahama Umar Kwaru ‎ ‎ ‎Wani bidiyo da ya fara yawo...

Allah ya yi wa Kanal Daudu Sulaimanu Rasuwa

Daga Jafar Adam   Allah ya yiwa Kanal Daudu Sulaiman Rasuwar...