Zanga-zanga ta ɓarke a Ghana inda ake zargin ƴan Najeriya da aikata laifukan kisan gilla da karuwanci.
Shafin RFI na X ya rawaito cewa masu zanga-zangar na neman a kori ƴan Najeriya daga kasar.

Masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa ƴan kasuwan Najeriya na mamaye mus kasuwanni tare da karya dokokin na kasuwanci .
Wakilin RFI a Ghana, Abdallah Sham-un Bako ya zagaya babar kasuwar circle dake Accra inda anan ne yawancin yan najeriya ke gudanar da kasuwancin su.