Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da bincike kan ƙorafin da wasu manoma ke yi na zargin shugabancin ƙaramar hukumar Tudun Wada karkashin jagorancin Hajiya Sa’adatu Yusha’u, kan kwace musu gonakinsu da ke Dajin Gurfa a karamar hukumar ta Tudun Wada a Kano.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Alhaji Lawan Hussain Cediyar ƴan Gurasa ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan amsa gayyatar da Majalisar ta yi wa kungiyar da ke rajin kare hakkin Ɗan-adam da tabbatar da daidaito a cikin al’umma wadda ta aike wa Majalisar korafin Manoman.
Da ya ke jawabi bayan amsa gayyatar da Majalisar ta yi musu, shugaban kungiyar Sa’id Bin Usman, ya ce akwai tarin korafe-korafe kan dambarwar hakkin mallaka na gonaki tsakanin shugabancin karamar hukumar Tudun Tada da kuma manoman yankin.
Manoma da dama ne a Dajin na Gurfa da ke yankin karamar hukumar Tudun Wada suka shigar da korafin su kan zargin shugabar ƙaramar hukumar da ƙwace musu Gonakin su, in da kuma suke fatan majalisar dokokin jihar kano da ta duba kokensu domin samar musu da adalci.
Freedom Radio