Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari, marigayi shugaban Najeriya.
Tinubu ya sanar da haka ne a taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

“Kafin mu fara addu’o’i domin karrama Buhari, ina sanar da ku cewa mun sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari,” in ji Tinubu.
Manyan jami’an gwamnati da dama ne suka halarci taron addu’o’in, ciki har da wasu daga cikin ƴaƴan marigayin.