A halin yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na wata ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro da kuma babban sufeton ƴansanda na kasa (IGP) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
DAILY TRUST ta rawaito cewa wadanda su ka halarci ganawar sun hada da babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa; Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede; Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da Sufeto Janar na ƴansanda, Kayode Egbetokun.
Ko da ya ke ba a fayyace cikakken bayanin taron ba har zuwa lokacin da Trust ta buga labarin, amma tattaunawar ba za ta rasa nasaba da sabbin hare-haren ƴan ta’adda a wasu sassan kasar ba.