Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu daga jihar Kano sun sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun sauya sheƙar a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis.

Wadanda suka sauya shekar su ne Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo, wakilan mazabun Rano/Bunkure/Kibiya da Karaye/Rogo a jihar Kano.
‘Yan majalisar sun bayyana rikicin cikin gida da jam’iyyar NNPP ke fama da shi a matsayin dalilin sauya shekar su.