Daga Rabi’u Usman
Al’ummar ya garin Bechi dake cikin karamar hukumar Kumbotso sun koka akan yadda su ke zargin za’a kwace musu filin Makarantar Sakandaren ‘yan mata da Gwamnatin Kano Karkashin Ma’aikatar Ilimi ta fara gina musu Aji a cikin sa.
Kwamatin Samar da Cigaban yankin Bechi da kewaye (BECHI COMMUNITY DEVELOPMENT ASSOCIATION) ne su ka yi kira ga Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf akan Matakin da wasu Mutane da kawo yanzu ba’a san daga inda suke ba, suke kokarin yanka Filin (Awon Igiya) domin siyarwa Jama’a.

Inda suka ce, an samar da Filin ne tun lokacin mulkin tsohon Gwamnan kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso Zango na biyu a shekarar 2014 domin gina Makarantar Sakandaren ‘yan mata sakamakon Aron makarantar primary da a kayi.
Wanda primary din ake gudanar da ita daga wani lokaci da Safe zuwa wani lokaci a tashesu domin ‘yan sakandare su yi nasu Karatun.
Sunce, Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano ta amince da Gina Makarantar Sakandaren ‘yan mata a yankin tare da basu Cikakkiyar Shaidar fara ginin, wanda har an fara Gina aji guda amma daga bisani sai suka wayi gari ‘Dan kwangila ya kwashe kayan aikin sa ya tafi ba tare da an Sani ba.
Hakan ne ta sa wasu mutane su ka shiga yankin nasu suka fara yunkurin yanka Filin makarantar zasu fara saidawa jama’a a matsayin fulotai.
A hannu guda Suma, kwamatin Iyaye da Daliban makarantar primary da Sakandaren ‘yan mata a yankin Bechi ta Bakin Shugaban kwamatin SBMC Comrade Adamu Bechi, ya roki Mahukunta musamman gwamnatin kano tayi bincike akan yanda aka fara Gina Makarantar Sakandaren ‘yan matan amma aka Dakatar.
Wanda hakan ya janyo Babban kalubale ga makarantar da al’ummar yankin garin Bechi da kewaye na rashin samun Ilimin ‘yaya Mata.
A don haka su ka nemi daukin gwamnatin kano ta dubi halin da Ilimin ‘yaya Mata yake ciki a yankin nasu, wanda a cewar su, har Makobtan Unguwannin dake kewaye dasu suna zuwa makarantar.