NUJ ta kaddamar da kungiyar kafafen yada labarai na yanar gizo a Kano

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ ta kaddamar da reshen kungiyar kafafen yada labarai ta yanar gizo wato Kano Online Media Chapel kamar yadda kundin tsarin mulkin NUJ ya tanada.

A yayin kaddamar da gidan reshen kungiyar na Kano Online Media Chapel, shugaban kwamitin kaddamarwar wanda ya ke gogaggen dan jarida ne sama da shekaru hamsin, Alhaji Ahmad Aminu, ya shaidawa mahalarta taron cewa kafafen sada zumunta na zamani suna da alaka da fasahar sadarwa da sadarwa. Ya kuma yabawa ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano karkashin Kwamared Ibrahim Waiya bisa kokarin da take yi na ganin ‘yan jaridun yanar gizo sun kasanace karkashin inuwa daya.

Alhaji Ahmad Aminu ya bukaci kafafen yada labarai na yanar gizo da su rika yada bayanai masu inganci, da amfani ga al’umma. Ya kuma jaddada muhimmancin yin aiki tare da tsakanin kafafen yada labarai na yanar gizo da gidajen Radio da Talabijin da ke da ake da su sama da 30 a Kano.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Shahararren dan jaridan ya bayyana cewa daya daga cikin manyan kalubalen da Kano ke fuskanta shi ne yaren yadda wasu suke amfani da kafafen yada labarai ba yadda ya dace ba. Ya koka da yadda Kano ta yi kaurin suna cin zarafin al’umma a kafafen yada labarai sabanin jihohin da ke makwabtaka da jihar Kano.

Da yake nasa jawabin Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa ya jima yana baiwa aikin jarida goyon baya, kuma ya sake nanata hakan tare da yin alkawarin ba da duk wata gudunmawa da ake bukata don inganta aikin a jihar Kano.

Da dumi-dumi: Sarki Aminu ya nada sabon Galadiman Kano

Nigerian Tracker ta ruwaito cewa Kwamared Ibrahim Waiya ya bayyana cewa ranar 27 ga watan Afrilu rana ce mai cike da tarihi saboda it ce ranar da aka kaddamar da reshen kungiyar NUJ na kafafen yada labarai na yanar gizo.

“Muna goyon bayan wannan tsari kuma muna da burin kawo gyara a bangaren yada labarai, abin da ke faruwa a kafafen yada labarai abin takaici ne, kuma ba za mu iya canza shi ba sai mun hada masu ruwa da tsaki, ba ma son a bar Kano a baya a wannan tafiyar.”

An samar da wannan kungiyar ne saboda dukkanin masu aikin yada labarai ta yanar gizo, don haka ina kira ga dukkaninsu da su yi rijista da kungiyar domin ta haka ne gwamnati zata iya tallafawa musu.

A nasa bangaren, sabon shugaban kungiyar kafaden yada labarai na yanar gizo a Kano wato Kano Online Media Chapel, Kwamared Abubakar Abdulkadir Dangambo wanda shi ne mawallafin jaridar Independent Post ya bayyana jin dadinsa da kuma alkawarin hada kan ya’yan kungiyar.

InShot 20250309 102403344

Ya ce kafa kungiyar kafafen yada labarai ta Kano Online Chapel wani yunkuri ne na matakin cigaba, wanda za su mai da hankali wajen yada labarai masu nagarta. Ya ce ba a samar da kungiyar da ta zamo kishiyar sauran kafafen yada labarai ba .

Dangambo ya ce a matsayinsa na shugaba bai zai yi duk mai yiwuwa don samar da cigaba ga kungiyar tare da kare kima da martabar ya’yan kungiyar.

Sabbin shuwagabannin kungiyar kafafen yada labarai na Kano Online da aka kaddamar sun haɗa da:

– Shugaba: Abubakar Abdulkadir Dangambo (Independent Post)

– Mataimakiyar Shugaba: Kahdija Aliyu (Paradigm News)

– Ma’aji: Abbas Yushau Yusuf (Nigeria Tracker)

– Sakatare: Isyaku Ahmad (Stallion Times)

– Auditor: Musa Ahmad Durumin Iya (Alifijir labarai)

– Mataimakiyar Sakatare: Zahrau Nasir (Daily Watch 24)

– Sakatariyar Kudi: Zainab Abdurrahman Mai Agogo (Kakaki24)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Shari’a ta Kano ta Gargadi Alkalai 2, ta kuma dakatar da Magatakarda 2

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Hukumar kula da shari’a ta jihar...

Amarya Aisha Humaira ta aike da sako ga masu kage kan alakarsu da Rarara

  Aisha Humaira, amaryar kuma abokiyar aikin mawaki Dauda Kahutu...

Da dumi-dumi: Sarki Aminu ya nada sabon Galadiman Kano

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Mai Martaba Sarkin Kano na 15,...

Kwanaki 100 Waiya a Ofis: Shin An Sami Riba Kuwa?

Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa   A makon da mu ka yi...