Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alh. Aminu Ado Bayero ya nada dan uwansa kuma babban dan Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero wato Alh. Sanusi Ado Bayero a matsayin Galadiman Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata Wasika ta sanar da nadin da Masarautar kano ta turawa Alhaji Sanusi Ado Bayero wadda jaridar Kadaura24 ta gani a yammacin wannan rana.

Wasikar mai kwanan watan 21 ga wannan watan Nan, wadda Alh. Awaisu Abbas sanusi ya sanyawa hannu, ta ce Sarkin ya amince da daga likafar Alhaji Sanusi Ado Bayero daga Wamban Kano zuwa Galadiman Kano.
Hajjin Bana: An sanya ranar da Alhazan Kano za su fara tashi zuwa Saudiyya
Wasikar ta ce za a gudanar da bikin nadin ne a ranar juma’a 02 ga watan Mayu 2025 a fadar Sarkin dake gidan Sarki na Nasarawa.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a kwanakin baya ne dai Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi ya rasu.
Sai dai bayan rasuwar ta sa Sarki Sanusi II shi ma ya nada sabon Galadiman, yanzu kuma ga shi shi ma sarki Aminu zai nada nashi sabon Galadiman, wanda hakan ke nuna cewa rikicin Masarautar kano na nan.