Yadda Ganduje ya karbi Kawu Sumaila, Rurum, Baffa Bichi, Rogo da wasu bayan ficewarsu daga NNPP

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Shugaban jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje CON ya karbi jiga-jigan jam’iyyar NNPP wadanda su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Daga cikin wadanda Abdullahi Umar Ganduje ya karba sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Baffa Bichi da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta Makoda, Hon. Badamasi Ayuba.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sauran sun hada da Hon. Abdullahi Sani Rogo da Rt. Hon. Zubairu Hamza Masu da Hon. Muhammad Diggol da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da Hon. Abbas Sani Abbas.

A Gaggauce: Sanata Kawu Sumaila ya fice daga NNPP zuwa APC

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin Ganduje Aminu Dahiru Ahmad ya aikowa Kadaura24.

Sanin kowa ne a lokuta daban-daban an jiyo wadannan jiga-jigan jamiyyar NNPP su na bayyana irin rashin adalcin da jagoran jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya Dr Rabi’u Kwankwaso ya ke musu.

Wannan dalili da ma wasu dalilai yasa su ka fice daga jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar APC mai albarka.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a jiya Laraba ne Kawu Sumaila ya fice daga jam’iyyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...