Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta kasa NBC da masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a kafafen yada labarai don magance yadda wasu ke amfani da kafofin wajen cin zarafin al’umma ko kuma bata musu suna.
Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin yaron wayar da kan masu shiga kafafen yada labaran don yin magana ta siyasa, kan irin kalaman da za su yi amfani da su.

Waiya, ya kuma ce gwamnatin Kano ba wai tana nufin hana mutum fadin albarkacin bakinsa bane, ana so ne dai a magance yadda wasu ke fakewa da hakan wajen cin zarafin al’umma.
” Mun shirya wannan bita ne don mu fadakar da ku illolin da ke tattare da cin mutuncin mutane da yi musu kazafi da sunan adawa ko Siyasa, inda ya ce duk mai kishin Kano ba zai aminta da wannan abun ba” Inji Waiya
A Gaggauce: Sanata Kawu Sumaila ya fice daga NNPP zuwa APC
Ya ce gwamnatin Kano ba ta da wani nufi da hana yi mata adawa, amma ta damu matuka da yadda ake cin mutuncin masu mutunci don haka mu ke son kawo karshen Wannan dabi’ar.
Da yake jawabi Dakta Bashir Aliyu Umar babban limamin masallacin juma’a na alfurkan dake Nasarawa GRA cewa ya yi, duk abin da mutun ya fada da yake ba nagaskiya bane sai Allah ya biwa wanda akaiwa kazafin hakkinsa a ranar gobe alkiyama.
Shi kuwa shugaban kungiyar masu magana a kafafen yada labarai a nan Kano (Gauta Club) Alhaji Hamisu Danwawu Fagge cewa ya yi shirya taruka irin wadan nan zai sa a samu gyaran da ya kamata ga mutanan dake magana a kafafen yada labarai.
Za a kwashe kwanaki biyu a na gudanar da taron karawa juna sanin da ma’aikatar yada labaran ta shirya hadin gwiwa da hukumar dake lura da kafofin yada labarai ta kasa NBC shiyyar Kano.
Haka zalika taron ya samu halartar Muhammad Sulaimanu Gama da ya fara gabatar da shirin siyasa mai suna Gauta a nan Kano da kuma masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a nan Kano harma da masu magana a kafafen yada labaran da dai sauran su.