Rashin wuta: Mazauna Lokon Makera na cigiyar yan majalisun jiha da na tarayya na Gwale

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Al’ummar unguwar Lokon Makera dake karamar hukumar Gwale dake cikin kwaryar birnin Kano sun koka bisa yadda su ka shafe sama da kwanaki 33 ba tare da samun hasken wutar Lantarki ba.

A zantawar jaridar Kadaura24 da guda cikin Malaman Addinin musulunci a yankin Malam Muhammad Dauda lokon Makera, ya ce sun shiga wannan halin ne sakamakon lalacewar Injin da ke baiwa unguwarsu hasken wutar lantarki.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Malamin ya ce abin takaici ne yadda mutanen yankin su ke fama da matsalar wuta tun cikin Azumin watan Ramadan har zuwa yanzu kuma an kasa samun wanda zai warware musu matsalar cikin yan Siyasar dake karamar hukumar.

Malamin ya yi zargin nuna halin ko-in-kula daga shugabanni yankin musamman yan siyasa da su ka hada da Yan majalisar tarayya da takwaransa na majalisar dokokin Jihar Kano ya na mai cewa “mafi yawan al’umma ba su ma san wadanda ke wakiltarsu a yankin ba kuma cikinsu harda ni duk da kasancewata malamin Addinin musulunci kuma dan boko”.

Yanzu-yanzu: Ganduje ya magantu kan batun komawar Kwankwaso APC

” Mun rasa inda za mu sami dan majalisarmu na jihar da na tarayya ballantana mu kai musu kokenmu, don haka muna cigiyarsu su dubi Allah da ma’aiki su zo su cire mu daga wannan matsala”.

Dauda lokon Makera ya bukaci kamfanin rarraba hasken wutar Lantarki na jihohin Kano, Jigawa da Katsina KEDCO da ya kaiwa al’ummar yankin dauki.

InShot 20250309 102403344

Malamin ya ce matukar Yan siyasa a Gwale su ka gaza warware matsalolin da mutane ka fama da su akwai ranar kin dillanci, ranar da kwanne dan siyasa zai je da bukata kuma al’ummar su yi watsi da bukatarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...