Daga Kamal Yakubu Ali
Cibiyar Markaz Imamu malik da ke unguwar Dorayi farin masallaci bayan gidan sakin Dutse ta gudanar da rabon kayan abinchi ga mazauna yankin da su ka kai kimanin mutane 85 domin saukaka musu da kara kulla kyakyawar alaka kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Shugaban cibiyar ta Imamu malik malam Bashir Aliyu umar ya ce su na gudanar da rabon kayan abinchi ne a kowacce shekara ga magidanta masu karamin karfi da kuma iyayen marayu dake zaune a bayan gidan sarkin Dutse dake unguwar Dorayi.

Ya bayyana cewa al’ummar da ke yankin su ne suke tattara kudadensu kowa ya na bayarwa gwargwadon ikonsa, inda ake hadawa ake sayan kayan abinci da suka hadarda shinkafa, Taliya da kuma Gero, domin tallafawa alumma da suke rayuwa da su, karkashin kulawar cibiyar Imamu malik dake farin masallaci.
Da ya ke karin haske shugaban cibiyar malam Bashir Aliyu ya ce sun raba kayan ne don saukakawa al’umma , musamman a wannan lokaci da ake gudanar da ibadar azumin watan Ramadana.
Yanzu-yanzu: EFCC ta bayyana dalilan da su ka sa ta kama Jarumar Tiktok Murja Kunya
Ya kuma mika godiya ga dukkanin wadanda su casa ka bayar da tallafin kayan abinci da kudade a rabawa bayin Allah a wannan lokaci da Allah ya ke son bayinsa su rika gudanarda aiyukan alkhairi, muna addu’ar Allah ya sakawa kowa da Alkhairi .
Ya kuma yi kira ga sauran mawadata da su rika tallafawa al’umma, musamman a wannan lokaci na azumin Ramadana, domin Annabi sallallahu Alaihi wasalam idan azumin Ramadana yazo yana Rubanya kyautarsa fiye da yadda iska take kadawa.
Wakilin kadaura24 ya rawaito mana cewa kayan da aka raba sun hadar da Shinkafa Masara, Taliya da makaroni da dai sauransu.