Kungiyar kwallon kafa Barau FC ta dakatar mai horar da yan wasan ta Salisu Yusuf

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC ta dakatar da babban mai horar da yan wasan ta Salisu na tsahun wani lokaci nan take daga aikinsa.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar ta Barau FC Ahmad Hamisu Gwale ya sanyawa hannu, kuma mataimakinsa Ashiru Rabi’u Gidan Tudi ya aikowa Kadaura24.

Talla

Ya ce an dauki wannan matakin ne bayan taron da shugaban cin kungiyar ta gudanar sakamakon halin da take ciki a wannan kaka ta 2024-2025 na rashin samun nasarori a wasannin gida da waje.

Sanarawar taci gabata da cewa an yankin shawarar tabbatar da Rabi’u Tata, a matsayin wanda zai maye gurbin Salisu Yusif a matakin na rikon kwarya a dukkanin wasannin ta a nan gaba.

Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC dai na fafatawa ne a gasar Firimiya ta Najeriya mai daraja ta biyu NNL, inda yanzu haka take a cikin rukuni na C da ya fito daga yankin Arewawaci Najeriya.

Hakazalika cikin wasanni hudun data buga yanzu haka na dauke da maki biyu ne a cikin rukuni, yayin da a ranar Asabar zata karbi bakwancin kungiyar kwallon kafa ta Sokkoto United a wasa mako na biyar duka a cikin rukunin na C.

Daga karshe mahunkutan kungiyar ta Barau FC sun yaba da irin kokarin da Salisu Yusuf yayi, a lokacin da ye rike da kungiyar a tsahun wasannin da ya fafata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nan gaba kadan za mu bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya – Babban Hafsan tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce...

Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano

Gwamnatin Jihar Kano Hadin gwaiwa da Rundunar Yansandan Jihar...

Masu Mukamai a gwamnatin Kano ba su da uzurin kin taimakawa yan Kwankwasiyya – Sanusi Bature

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin...

Magoya bayan Barr Ibrahim Isa (Matawallen Gwagwarwa) sun aikawa Gwamnan Kano Budaddiyar Wasika

Daga Isa Ahmad Getso Kira don nemawa Barr. Ibrahim Isa...