Zaɓen ƙananan hukumomi: Gwamna Fubara ya Zargi Babban Sifeton Ƴansanda Nigeria da Yunkuri Tada Husuma a Rivers

Date:

 

 

Gwamnan jihar Rivers, Similanayi Fubara, ya bayyana cewa idan har aka samu karyewar doka da oda a jihar zai dora laifin hakan ga babban sufeto janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun.

Daily Trust ta rawaito yadda Fubara ya isa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Rivers a cikin daren Juma’a don hana yunkurin sace kayayyakin zaben kananan hukumomi da za a gudanar a gobe Asabar a jihar.

Talla

Da yake jawabi a yayin taron manema labarai a birnin Fatakwal a ranar Juma’a, Fubara ya gargadi babban Sufeton ‘yansandan da ya kula da rawar da yake takawa a matsayin sa na shugaban rundunar ‘yansanda.

Gwamnan ya bayyana cewa babban aikin ‘yansanda shi ne kare lafiya da dukiyoyin al’umma, ba wai mamaye ofishin hukumar zabe ba.

Zaɓen ƙananan hukumomi: NNPP ta sauya dan takarar ciyaman a Kano

“Ina fadin wannan anan, IGP ya sani cewa duk wani abu da zai haifar da karya doka a wannan jihar, ina tunanin a karshe, ya shirya daukar alhakin hakan.

Talla

“Da safiyar yau, na samu rahotan tsaro dake cewa ‘yansanda sun mamaye ofishin hukumar zabe. Na yi matukar mamaki saboda kafin wannan lokacin na samu bayanin janye masu tsaron hukumar. Shi yasa naje wajen tunda mallakin gwamnatin jihar Rivers ne”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NURTW ta Karrama DMD Karota Auwal Aranposu

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar...

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...