Daga Rabi’u Usman
Gwamnatin jihar kano ta bayar da kayayyakin kula da kiwon lafiya ga masu larurar laka a nan jihar da kudin su ya tasamma sama da naira miliyan bakwai tare da basu tallafin kudi naira miliyan 1 domin gudanar da bikin zagayowar ranar masu larurar laka ta duniya.
Kwamishiniyar ma’aikatar mata, kananan yara da masu bukata ta musamman Hajiya Aisha Lawan Saji Rano ce ta bayar da kayayyakin ga Kungiyar masu larurar laka a shalkwatar ma’aikatar mata kananan yara da masu bukata ta musamman da yammacin ranar alhamis.

Kayayyakin da aka bayar sun hadar da keken zama (Wheel chair) guda 20, audugar mata, man tsabtace hannu, katata, bandeji da kayan dressing harma da zunzurutun kudi naira miliyan 1, da dai sauran su.
Bayan kammala taron ne wakilin mu ya zanta da kwamishina Aisha Lawan saji akan yanda aka gudanar da rabon kayan.
Kwankwaso ya karɓi yan APC sama da 960 zuwa jam’iyyar NNPP a Kano
Inda ta bayyana cewar, gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya sahale wa ma’aikatar ne domin mata, kananan yara da masu bukata ta musamman suma su san gwamnatin kano tana damawa da su.
Ta kara cewar, mutane da yewa musamman masu bukata ta musamman da masu larurar laka suna zuwa ma’aikatar suna ki koken su na rashin irin wadannan kayayyakin na amfanin yau da kullum.
Don haka gwamnan ya bayar da umarnin a samar musu da abinda ya sawwaka domin a rage musu radadin Damunar su.

A nasu bangaren Wasu daga cikin mutanen da suka amfana da tallafin musamman shugabancin Kungiyar masu bukata ta musamman bangaren masu larurar laka, sun bayyana Jin Dadin su sakamakon yanda suka ce sun dade suna neman me share musu hawaye akan damuwar su tare da neman wadannan kayayyakin amma basu da kudin Siya.

Sai ga shi rana tsaka gwamnatin kano ta biya musu bukatun su wanda suka dade suna nema.
A karshe sunce nan da 1 ga watan December zasu gudanar da bikin zagayowar ranar masu larurar laka wanda majalisar Dinkin Duniya take warewa sannan su baiwa mambobin Kungiyar musamman wadanda suke da bukata.