Zaɓen kananan hukumomi: APC na zargin gwamnatin Kano

Date:

 

Jam’iyyar APC na zargin Gwamnatin NNPP a Jihar Kano da yunƙurin karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi domin gudanar da zaɓensu da ke tafe.

Shugaban APC a Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar tana ƙoƙarin karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi domin ɗaukar nauyin ’yan takarar NNPP a zaɓen.

 

Talla

Abdullahi Abbas ya bukaci Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin Kasa (EFCC) da takwararta ICPC su sanya ido sosai a kan ma’aikatar ƙananan hukumomin jihar game da wannan lamari.

Yan APC Sama da 1,300 sun fice daga jam’iyyar zuwa NNPP a Dawakin Tofa

“Muna sanar da EFCC da ICPC cewa bayan rushe shugabannin riƙon ƙananan hukumomi, ma’aikatar tana ƙoƙarin amfani da Daraktocin Kula da Ma’aikata, waɗanda ma’aikatan gwamnati ne da ke da alhakin kula da kuɗaɗe, da zummar amfani da kuɗaɗen al’umma wajen gudanar da zaɓen.

Talla

“Ya kamata EFCC ta binciki asusun ƙananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano domin tabbatar da ba a karkatar da kuɗaɗensu ba,” in ji Abdullahi Abbas.

Talla

Ya ƙara da neman EFCC ta gayyaci shugabannin riƙon ƙananan hukumomin jihar da aka rushe, kowanensu ya bayar da bayanan kuɗaɗen da ya bari.

Su kuma Daraktocin Kula da Ma’aikatan da aka miƙa wa ragama su kawo bayanan yadda suka sarrafa kuɗaɗen da suka gada daga shugabannin riƙon, domin daƙile karkatar da su wajen zuwa zaɓen ƙananan hukumomin.

Ya ce hakan na da muhimmanci, la’akari da zargin da ake wa tsohon gwamnan jihar kuma jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na karkatar da Naira biliyan 30.8 daga asusun ƙananan hukumomi domin zaben shugaban ƙasa a shekarar 2015.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar cigaban Ilimi da gyaran tarbiya ta unguwar zango ta shirya taron kan tarbiyya da tsaro

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malami a jami'ar Bayero dake...

Gwamnatin Kano ta sanar da Ranar Fara hutun zangon Karatu na 3 ga ɗaliban jihar

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da...

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...