Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban kamfanin shinkafar Gerawa rice meals ya Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya kaddamar da fara biyan ma’aikatan kamfanin mafi ƙaranci albashi na Naira 70.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa tuni shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa dokar mafi ƙarancin albashin hannu bayan majalisa ta amince da dokar.
Yayin wani taro da aka shirya wanda ya sami halartar dukkanin ma’aikatan kamfanin a harabar kamfanin dake hadejia road a Kano, Shugaban rukunonin daraktocin kamfanin Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya ce an kaddamar fara biyan mafi ƙarancin albashin ne domin cika ka’idar doka da kuma kyautatawa ma’aikatansu.
Sojoji Sun Sako Seaman Abbas Bayan Shekaru 6 A Tsare
” Mun Shirya tsaf domin yin duk wani abu da zai kyautatawa ma’aikatanmu, domin Mun dauki Jin dadin ma’aikatan mu da matukar muhimmaci saboda gudunnawar da suke ba mu, ta yin aiki tukuru domin ci gaban kamfanin mu”. Inji Gerawa
Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa wanda Manajan Daraktan kamfanin na Gerawa Alhaji Muhammad Isyaku ya wakilta ya sake yiwa ma’aikatan kamfanin albishirin cewa bayan biyan mafi ƙarancin albashin kamfanin zai kuma baiwa ma’aikatan kyautar rabin albashinsu har na tsahon watanni biyu da suka gabata.
” Bayan wannan Kuma Mun yi tanadi kyauta mai tsoka ga duk ma’aikatacin da ya fi nuna kwazo a warin aikin don kara masa kwarin gwiwa da kuma zaburar da abokan aikinsa kwatan-kwacin yadda al’qur’ani yace sakamakon kyakykyawa shi ne kyakykyawa”. A cewar Alhaji Ibrahim Gerawa
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran kamfanin Gerawa Group of Company Kwamaret Babangida Mamuda Biyamusu ya aikowa kadaura24, ya ce Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya bukaci ma’aikatan da su zage damtse wajen yin aiki tukuru duba da yadda kamfanin ya kyautata musu.