Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kungiyar ma’aikatan radio da talabijin ta kasa reshen jihar kano RATTAWU ta ba da tabbacin hada kai da kungiyoyi NUJ da NAWOJ domin cigaban mambobinsu da jihar kano baki daya.
” Aikin mu iri daya ne kuma muna aiki tare to ya kamata mu shugabannin waɗannan kungiyoyi mu hada kan mu, mu dauka duk abun da ya shafi dayanmu ya shafemu duk, tabbas idan muka yi haka zamu sabi gagarumar nasara”.
Shugaban kungiyar ta RATTAWU reshen jihar Babangida Mahmoud Biyamusu ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci shugabannin kungiyarsu domin taya sabbin Shugabannin kungiyoyin NUJ d NAWOJ murnar lashe zabukan da suka yi a yan kwanakin baya.
Muhimmiyar sanarwa daga gwamantin jihar kano ga wadanda suka yi takara a NNPP
Ya ce idan shugabannin kungiyoyin suka cire ban-ban-bancen dake tsakanisu su za su samar da cigaba da mambobinsu da kuma jihar kano baki daya.
Shugaban na RATTAWU ya mika takardun taya murna ga sabbin Shugabannin NUJ d NAWOJ, Sannan ya horesu da su zamo masu gaskiya da rikon amana.
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar kano Sulaiman Abdullahi Dederi ya godewa shugabannin na kungiyar RATTAWU bisa ziyarar taya murna da ya kai musu har Ofishinsu dake sakatariyar yan jaridu ta kano.

” Ina baka tabbacin za mu hada kai, kuma za mu yi aiki tare domin sai da hadin kai Sannan ake samun kowacce irin nasara, kuma dama da dan NUJ dana RATTAWU ko NAWOJ ko SWAN duk daya ne, kawai kundin tsarin mulkin kungiyoyin ne ya raba mu a wasu aiyukan, amma duk da haka zamu yi aiki tare don cigabanmu baki daya”. Inji shugaban NUJ na Kano.
Itama a nata bangaran shugabar Mata yan jaridu ta kasa reshen jihar kano Bahijja Malam Kabara ta ce wannan ziyarar wata yar manuniyace dake nuna cewa dukkanin kungiyoyin sun shirya yin aiki tare domin cigaban mambobinsu.
Bahijja kabara ta kara dace wa za su yi aiki kafada da kafada domin ciyar da aikin jarida gaba a jihar kano da kasa baki daya.
Haka kuma tayi kira da gwamnatin jihar kano da ta ci gaba da basu hadin kai yadda ya kamata badan komai ba sai don ganin an cigaba da bunkasa aikin ya jarida a jihar kano da kasa baki daya.
Ga hotunan yadda taron ya Kasance