Bai dace matasa su rika fita Takutaha da kayan da basu dace ba – Dr. Muhammad Khamis

Date:

Daga Idris Usman Rijiyar lemo

 

Babban limamin masallacin Juma’a na Jaami’ul Khairi sheikh Abdullahi Aujara dake Kwaciri Sabuwar Fagge, kuma malami a sashin koyar da harsuna a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Dr Muhammad Khamis Husaini, ya ja halin masa da su guji yin shigar da bata daceba a ranar bukukuwan takutaha.

Ya bayyana takaicin sa da samun karuwar masu yin shigar kazanta da rawar DJ da kuma cakudedeniya tsakanin maza da mata da sunan nuna soyayya ga Annabi a ranar Takutaha.

Dr. Muhammad khamis ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da ya aikowa kadaura24 ranar asabar.

Muhimmiyar sanarwa daga gwamantin jihar kano ga wadanda suka yi takara a NNPP

” Bai da ce ace an sami masoyin Manzon Allah Sallahu alaihi wasallam da yin abubunwan da basu dace ba, kuma a wajen taron murnar zagayowar ranar sunan shugaban Halitta”.

Ya ce masu nuna wannan dabi’a suna jawa addinin Musulunci da Musulmi zage a wajen makiyan sa.

Talla

Yace nuna soyayyar annabi ta gaskiya ita ce yin amfani da dukiyoyi wajen raba sadaka ga mabukata da sassauta farashin kayayyakin masarufi ga takalawa da kuma tausayawa gajiyayyu da aikata sauran aiyukan alkhairi da nuna tausayi a ranar ta takutaha.

Daga bisani malamin jami’ar ya bukaci gwamnatin Kano, da take bayar da katin gayyata ga malamai daga bangarori daban-daban a ranar Takutaha domin haduwa a yiwa jihar Kano da Kasa addu’ar neman samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali da karuwar tattalin arziki mai yalwa da kuma ci gaba da mai dorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu

  Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya...

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta yi Sabon Shugabanta na Kasa

  Ministan Jinkai da ba da Agajin Gaggawa, Farfesa Nentawe...

Ku shiga harkokin Kasuwanci domin akwai albarka a ciki – Sarkin Kabin Jega ga matasa

Daga: Ibrahim Sidi Mohammad Jega Sarkin Kabin Jega, Alhaji Muhammad...

Kotua a Kano ta yankewa G-Fresh hukuncin zaman gidan yari

Kotu ta aike daAbubakar Ibrahim G. Fresh gidan gyaran...