Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Tsohon shugaban Jami’ar karatu daga gida ta Nigeriya wato (National Open University of Nigeria) Farfesa Abdullah Uba Adamu ya ce matakin da gwamnatin jihar kano ta dauka na soke jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi komawa baya ne ga kano da al’ummar jihar baki daya.
“Ba yadda za a yi ace wannan ci gaba ne, sai dai ace ci baya ne ga harkar ilimi, saboda idan aka ce duk gwamnatin da ta zo zata rushe cigaban da gwamnatin da ta gabace ta ta kawo, kawai saboda adawar siyasa to ba za a taba samun cigaba ba”.
Farfesa Abdullah Uba Adamu ya bayyana hakan ne a ga hira da yayi da gidan Radio freedom dake jihar kano a Arewacin Nigeria.
Dalilin da yasa gwamnatin Kano ta rushe Jami’ar ilimi ta Sa’adatu
Yace kamata yayi gwamnatin jihar kano ta zauna da ga me yasa ita gwamnatin da ta gabata ta daga darajar Kwalejin zuwa jami’an, idan dalilan masu kyau ne sai a bata ta, idan babu wasu kwararan dalili sai a mayar da ita ta koma matsayinta na Kwaleji, amma idan akwai kwararan dalilai to bai kamata a dawo da jami’ar baya ba sabada adawar siyasa ba.

“Jihar Kano ta na da jami’o’i da dama yanzu, wannan jami’o’in irii-iri ne, akwai na gwamanti akwai masu zaman kansu, saboda talakawa ba su da wata jami’an da zasu yi tunkaho da ita kamar jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi, yanzu mayar da ita Kwaleji an kaskantar da ita an kuma kaskantar da ilimin da yara suke samu a cikinta”. Inji Farfesa Abdullah Uba Adamu
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin jihar kano ta ce ta dawo da jami’ar matsayinta na baya na Kwalejin horar da malamai, a yayin zaman majalisar zartarwar jihar wanda gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.
Gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ce dai ta daga likkafar Kwalejin zuwa jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi.