Farashin man fetur: NNPC ta baiwa Matatar Ɗangote dama

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC, ya ce ba shi da ikon yankewa matatar mai ta Dangote da sauran matatun mai na gida farashin man fetur din da su ke tacewa.

Kamfanin mai na NNPC ya ce matatar Ɗangote da duk wata matatar cikin gida suna da ‘yancin siyar da man su kai tsaye ga ‘yan kasuwa akan farashin da suke so, yace hakan ne tsarin da ake yi yanzu a Nigeriya mai ya yiwa kansa farashi a kasuwa.

Mista Olufemi Soneye, Babban Jami’in hulda da jama’a na Kamfanin, NNPC Ltd. ne ya bayyana haka ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24, yayin da yake mayar da martani ga zargin kungiyar kare hakkin Musulmin Nigeria MURIC na cewa kamfanin na NNPC yana yiwa matatar Dangote zagon kasa.

Dalilin da yasa mai magana da yawun Shugaban ƙasa Tinubu ya Ajiye aikinsa

“An jawo hankalin NNPC Ltd. kan wata sanarwa da kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta fitar, inda ta ke zargin NNPC da yiwa matatar Dangote zagon kasa .

MURIC ta ce kamfanin NNPC ya zama shi kadai ya ke siyar da duk wasu kayayyaki da matatarDangote take fitarwa

Soneye ya ce kasuwa ce zata yiwa duk wani man fetur farashi ba iya na matatar Ɗangote ba har da sauran matatu na gida Nigeria da muke da su.

Ya ce sauye-sauyen da aka samu a farashin man fetur na baya-bayan nan ba shi da wani tasiri ga matatar Dangote ko wata matatar cikin gida ta shiga kasuwannin Najeriya.

Yadda za ku sayi Shinkafar Tinubu akan Naira dubu 40 kowanne buhu

“A gaskiya, idan ana ganin farashin yanzu yayi tsada, to ai dama ce ga kowacce matatar mai ta sayar da kayanta a farashi mai rahusa a kasuwannin Najeriya.

Ya ce kungiyar MURIC a matsayinta na kungiyar ya kamata ta tabbatar da gaskiyar lamari kafin ta yi tsokaci akai, domin tsokacin da ta yi cike yake da kura-kurai kuma zai iya harzuka yan Nigeriya su rika ganin bakin NNPC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...