An ƙayyade kuɗin fom din tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta ƙayyade kuɗin sayen fom ɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar a bana.

Shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da hakan ne a yayin bayyana jadawali da ƙa’idojin shiga zaɓen a wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a Kano a ranar Alhamis.

A yayin taron, hukumar zaɓen ta sanar da cewa duk mai son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma a zaɓen to zai sayi fom a kan naira miliyan 10.

A karon farko Farashin Kayan Abinchi ya sauka a Nigeriya

Yayin da ɗan takarar kansila kuma kuɗin fom ɗinsa ya kama naira miliyan biyar a cewar Farfesa Malumfashi.

Haka kuma, daga cikin ƙa’idojin shiga zaɓen dole ne ɗan takarar kujerar shugaban karamar hukuma ya kasance shekarun haihuwarsa sun kai 30 ko fiye, yayin da ɗan takarar kansila tilas ne ya kasance ya kai shekara 25 zuwa sama.

Yadda aka bankado haramtattun matatun man fetur 63 a Nigeria

Kazalika, Farfesa Malumfashi ya ce sai an yi wa kowanne ɗan takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi gwajin ƙwaya kafin a ba shi damar tsayawa takara.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar zaɓe wadda ta yi gargadi kan gujewa duk wani lamari da zai tayar da hargitsi, ta ce za a buɗe ƙofar soma yaƙin neman zaɓe daga ranar 6 ga watan Satumba sannan a rufe a ranar 31 ga watan Oktoban bana.

Farfesa Malumfashi ya nanata cewa ba za su lamunci duk nau’i na rashawa ba kuma duk wanda aka samu da yunƙurin bayarwa ko karɓar cin hanci za a tona masa asiri sannan ya fuskanci hukuncin da aka tanadar.

Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar ne a ranar 30 ga watan Nuwambar 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta...