Waɗanda Suka Yi Zanga-Zanga A 2012 Na Kokarin Danne Haƙƙin Yan Nigeria — Atiku

Date:

Daga Samira Ahmad

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙoƙarin dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 1 ga watan Agusta.

Atiku ya bayyana yunƙurin da abun dariya, saboda waɗanda ke ƙoƙarin hana zanga-zangar su ne waɗanda suka yi wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan zanga-zanga a shekarar 2012.

Zanga-zangar, wadda matasa suka shirya, na da nufin jawo hankali kan ƙaruwar yunwa da wahala da ’yan ƙasa ke fuskanta.

Talla
Talla

Masu shirya zanga-zangar sun ce za a shafe kwanaki 10 duba da halin matsi da ke ƙara ta’azzara, wanda suka ce akwai buƙatar kulawar gaggawa daga gwamnatin tarayya da na jihohi.

A wani rubutu da ya wallafa a sashin shafinsa na Facebook, Atiku ya jaddada cewa ‘yancin yin zanga-zanga yana cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kotu Ta Zauna Kan Shari’ar Kwankwaso Da EFCC

Ya buƙaci gwamnati da ta samar da yanayin tsaro da kwanciyar hankali don gudanar da zanga-zangar lumana, saboda ‘yan ƙasa suna da ’yancin gudanar da taro da bayyana ra’ayoyinsu.

Atiku ya soki gwamnati kan ƙoƙarin take waɗannan haƙƙoƙi, inda ya ce wannan ba ba ya cikin doka kuma yana barazana ga dimokuraɗiyya.

Ya ce gwamnati ya kamata ta mayar da hankali kan magance matsalolin da ke jawo yunwa da wahala maimakon ƙoƙarin hana zanga-zangar.

Idan ba a manta ba Shugaba Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su ƙaurace wa zanga-zangar tare da ba shi dama domin daidaita al’amura a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Daga Isa Ahmad Getso ‎ ‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana...

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

  Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin...

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   A karon farko an hadu tsakanin...

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...