Daga Isa Ahmad Getso
Yanzu haka Sakataren Gwamnatin Tarayya George akume yana ganawa da Ministocin da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribado akan batun zanga-zanga da ake shirin yi a Nigeria a wata mai kamawa.
Taron wanda ake yin sa cikin sirri sama da Ministocin gwamnatin Tinubu 40 ne suka halarta.
![Talla](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2024/07/IMG-20240701-WA0033-2-300x300.jpg)
Ministocin da suka halarci taron sun hadar da: Nyesom Wike (FCT), Yusuf Tuggar (Foreign Affairs), Zephaniah Jisalo (Special Duties), Tahir Mamman (Education), and Abubakar Bagudu (Budget and Planning).
Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma: Barau Jibril Ya Jinjinawa Tinubu
Sauran su ne Wale Edun (Finance), Mohammed Idris (Information), Bello Matawalle (Defence), David Umahi (Works), and the National Security Adviser (NSA) Nuhu Ribadu, da dai sauransu.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa wasu matasa a Nigeria ne suka shirya gudanar da zanga-zangar a duk fadin Nigeria, sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta a Nigeria.