Majalisa Ta Amince Da Kudirin Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata

Date:

 

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika kudurin karin mafi karancin albashi zuwa N70,000 ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

A ranar Talata shugaban ya mika kudurin karin albashin domin amincewar majalisa dokokin kasa kafin ya zama doka a fara biyan albashin.

Shugaban kasar ya bukaci majalisar ta hanzarta amincewa da kudurin na karin albashi, domin zama doka da kuma aiwatarwa.

Talla

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da takwaransa na Majalisar Wakilai Abbas sun samu wasikar kudurin da ke neman amincewar mambobin majalisun.

Abun da Mahukuntan Nigeria ke yiwa Matatar mai ta Ɗangote ka iya yiwa tattalin arzikin kasar illa – Falakin Shinkafi

N70,o00 shi ne mafi karancin albashin da shugaban kasar da kugniyoyin kwadago suka amince a kara daga Naira 30,000, bisa sharadin za a rika karawa bayan duk shekaru uku.

Shugaban kasan ya kuma aike wa majalisar da bukatar yin gyara ga dokar aikin dan sanda domin dacewa da Sashe na 58 na kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa gyaran fuska.

 

Gyaran da za a yi na da alaka da batun karfin ikon nadawa da kuma wa’adin shugaban ’yan sandan Najeriya.

Rahotanni da jaridar kadaura24 ta ke samu yanzu sun nuna cewa yanzu haka majalisar ta yi kudirin Karatu na daya dana biyu da na uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...