Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation GCAF Amb Auwalu Muhd Danlarabawa ne ya Bayyana haka a yau yayin Rabon kayan abinci ga iyayen Marayu Dake karkashin kulawar gidauniyar.

Amb Auwalu Muhd Danlarabawa yace al’umma na fama da Tsadar Rayuwa, sannan Kuma ga hauhawar farashi, ga Kuma kalu bale na rashin tsaro Dake addabar al’umma Musanman a Arewacin Kasar Wanda ya jefa al’umma da dama cikin tashin hankali na rabasu da Gidajen su, da gonakin su har Dan tarwatsa musu rayuwa.
Sannan ya Kara da ce mu Kalli yadda al’umma suka shiga wani yanayi kowa fafutuka yake Dan kawai ya samu abinci da zaici, wasu sai sunyi bara, wasu haka suke kwana su wuni, wasu Kuma sun kamu da cutuka, yayin da Kuma wasu ma sun mutu sanadiyyar damuwa, ciwon zuciya hawan jini yunwa da sauransu.
Kotu Ta Zauna Kan Shari’ar Kwankwaso Da EFCC
Lallai Muna Kira ga Gwamnati Wanda wannan hakkinta ne na samarwa yan kasa tsaro, kulawa da Kuma inganta rayuwar Dan Adam, da Kuma dokar kasa, ya zama wajibi Gwamnati tayi wani Abu da zai kawo karshen wannan yanayi kuma alumma su rayu cikin aminci da kaucewa fadawa ayyukan Ta’adanci a kasa.
Babu wata al’umma da zata zauna tana rayuwa a cikin kuncin Rayuwa face ta nemawa kanta mafita Mai kyau ko mara, kamar yadda muke gani Kullum ana fama da masu aikata laifuka daban daban Kuma idan an kamasu Babu wani Abu da suke cewa sai Kangin Rayuwa ne ya jefasu ga Aikatawa.

Muna fatan Gwamnati tun Daga Kan Gwamnonin mu, Yan majalisu da shugaban kasa zasu tashi tsaye Dan ganin talaka ya samu saukin Rayuwa Kuma Yana iya ciyar da kanshi abinci sannan ya samu tsaro yadda zaiyi noma da kiwo da walwala a zauna lafiya.
Amb Auwalu Muhd Danlarabawa
Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe
Grassroot Care and Aid Foundation GCAF