Rusau: Gwamnatin Kano Ta Bayyana Matsayarta Kan Gine-Ginen Dake Hanyar BUK

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani kan korafe-korafen da wasu masu kadarorin da ke kan hanyar BUK suka yi kan sanya musu gine-gine da ma’aikatar filaye da tsare-tsaren jihar ta yi.

Masu kadarorin dai sun koka kan matakin da suka bayyana a matsayin wani mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka na rusa ko kuma kwace musu kadarorin.

Daily Trust ta ruwaito cewa Ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta yi wa kaddarorin alama a ranar 10 ga Yuli, 2024.

Talla

A rusau din da aka yi a baya a jihar, gine-ginan na daga cikin wadanda aka shirya za a rushe, amma hakan bai yiwuwa ba sakamakon karar da aka shigar da gwamnati.

Sai dai al’amarin na baya-bayan nan ya baiwa masu gine-ginen mamaki inda suka yi kira ga gwamnati da ta duba matakin da take Shirin dauka .

Zanga-zanga: Tinubu ya bayyana sunan masu yunkurin kifar da gwamnatinsa

Ibrahim Mu’azzam, wanda yana daya daga cikin masu gine-ginen, ya ce, “Mun tashi ne muka ga wadannan jajayen fenti kamar yadda KNUPDA ta yi a bara. Mun yi iya kokarinmu amma abin ya ci tura daga baya muka kai kara. Har yanzu muna gaban kotu har zuwa yanzu da hakan ke faruwa.

“Tabbas mun samu wadannan gine-ginen ne a gwamnatin da ta gabata amma wadanda suka mallakesu na asali, sun mallakesu ne kusan shekaru 10 da suka wuce. Duk mutanen da a yanzu suka mallakin wuraren ba su ne wadanda gwamnatin ta basu ba.

“Lokacin da aka sayar mana da wannan wuri ya ma fi hadari. Saboda yan daba ne suke cin karensu babu babbaka a wannan wurin, ba irin aiyukan laifin da ba a aikatawa a wannan wurin.

Duk da bullar cutar kwalara, Makarantun Kano sun kasa daukar matakan kare ɗalibansu

Sai dai da yake mayar da martani game da koken, kwamishinan filaye da tsare-tsare, Abduljabbar Umar, ya ce gwamnati na kan bincike tare da duba yadda aka ba da wuraren kuma za a bayyana sakamakon nan ba da jimawa ba.

“Gaskiyar magana, wurin magudanar ruwa ne kuma akwai rafuka da ganuwa da aka samar tsawon shekarun da suka gabata wadanda suke da tarihi sosai a Kano. Tabbas, mun yi musu alama kuma hakan yana nufin akwai matsala . Ya zama wajibi mu kare tare da tabbatar da cewa an yi komai bisa tsar a babban birnin Kano.

“Mun sami koke-koke daga mazauna yankin game da wanzuwar wadannan gine-ginen da wasu mutane suka gina. Mun bincika kuma mun gani da kanmu.

“Mun shafe shekaru muna fama da matsalolin ambaliya wanda yana daya daga cikin illolin da gine-gine irin waɗannan suke haifarwa. Dukkanmu muna da alhakin kare muhalli. Mun yi namu bangaren kuma muna kan bincike kuma nan ba da jimawa ba za mu ga abin da za mu yi.”

Ya kara da cewa gwamnati ta al’umma ce kuma ba za ta yi wani abu da zai cutar da jama’a ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Karyata Rahoton Cibiyar Wale Soyinka Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton da...

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a...

Majalisar Kano ta buƙaci a soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan...

‎ ‎Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi

‎ ‎ ‎Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN),...