Zanga-zanga: Tinubu ya bayyana sunan masu yunkurin kifar da gwamnatinsa

Date:

 

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya zargi magoya bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023 da yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da fakewa da zanga-zangar nuna fushin ƴan Najeriya ga matsin rayuwa da ake fama da.

Onanuga ya yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da ya sanya a kan shafinsa sa ta X ranar Asabar.

Hotunan Yadda Sarki Aminu Ado ya yi fitar farko tun bayan fara rikicin masarautar kano

Sai dai bai bayar da wata hujja da za ta tabbatar da zargin nasa ba.

Talla

” Zanga-zangar da ake shiryawa a kasar nan, ba wani ne ke kulla shi ba illa tsohon ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, shi da makarraban sa ne ke kitsa wannan kisisina don a kifar da gwamnatin Tinubu

Kudu da Arewa duk kasa ana kira da a fito zanga-zanga saboda tsananin matsin rayuwa da ya addabi mutanen Najeriya.

Duk da bullar cutar kwalara, Makarantun Kano sun kasa daukar matakan kare ɗalibansu

Onanuga ya ce shekara ɗaya kacal Tinubu ya yi zuwa yanzu, sai a bari ya kammala shekarunsa huɗu tukunna, idan ya yi abin da ya dace sai a zaɓe shi ya zarce idan kuma ba haka ba sai aki zabarsa.

” Tattalin Arziki ya inganta, hauhawar farashin kayayyaki yana raguwa, an rage basussukan da ake bin kasa sannan hukumar FIRS ta kara yawan kuɗaɗen shiga da kasa ke samu kuma masu zuba jari sai tururuwa suke yi suna dawowa Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...