Daga Isa Ahmad Getso
Duk da karuwar bullar cutar kwalara a fadin Najeriya, har yanzu wasu makarantun gwamnati a Kano ba sa aiwatar da wasu matakan kariya daga cutar da ke barazana ga rayuwa dalibai.
Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai na baya-bayan nan, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli na Najeriya, Farfesa Joseph Utsev ya yi gargadi game da yiwuwar barkewar cutar kwalara yayin da jihohi 31 ke fuskantar hadarin barkewar cutar.
Har ila yau, Cibiyar Kula da Cututtuka masu saurin yaduwa ta Najeriya ta ce kasar ta sami rahoton mutane 1,528 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutane 53 a jihohi 31 na kananan hukumomi 107.
A Wata ziyara da wakilin jaridar Solacebase ya kai wasu makarantu da ke cikin birnin Kano, ta nuna yadda wasu makarantun ba sa daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar kwalara, lamarin da ke sanya yara kanana cikin hadarin kamuwa da cutar ta mai da gudawa.
SolaceBase ta ziyarci makarantun gwamnati guda shida a cikin babban birnin Kano, inda ta gano cewa makarantun ba su da tsaftataccen ruwan sha, saboda rijiyoyin burtsatse da suke su basa aiki, wanda hakan ya sanya matsugunan su cikin yanayi na kazanta.
Makarantun da suka ziyarta sun hada da Government Secondary School Stadium, Government Girls Senior Secondary School Kawaji, Government Secondary School Dabo, Dangana Government Senior Secondary School, Government College Kano, and Tudun Murtala Special Primary School.
Hotunan Yadda Sarki Aminu Ado ya yi fitar farko tun bayan fara rikicin masarautar kano
Bandakunan da ke cikin wadannan makarantu na da datti sosai, wanda hakan ke tilastawa dalibai maza yin bahaya a waje, su kuma ‘yan mata suna tsugunnon ne a cikin bandakunan masu dattin bandaki su yi fitsari ko bayan gida idan bukatar hakan ta taso, saboda ba bu yadda za su yi.
Halin da bandakunan suke ciki suna nuna karin hadarin kamuwa da cutar ga daliban dake makarantun .
Wasu daga cikin daliban da suka zanta da SolaceBase sun bayyana cewa ba su ma san cewa cutar amai da kudawa ta barke ba , wasu kuma suka ce a lokacin suka fara jin kalmar kwalara .
Musa Ibrahim daga makarantar GSS Stadium ya ce ya san kalmar amma bai san menene cutar ba.
Gwamnan kano ya bayyana dalilinsa na kin dawo da Sarkin Bichi
Ya kara da cewa, “Bandakunanmu na da datti sosai. Sakamakon haka, muke yin tsugunno a waje . Babu ruwa a makarantar ko da a bandaki, ballantana na’urar wanke hannu don tsaftace hannunmu.”
Wani dalibin GSS Dabo Mustapha Jibril ya bayyana cewa babu wani kokari da makarantar ta yi na hana daliban kamuwa da cutar.
Wata daliba daga makarantar Kawaji ta shaida wa wakilinmu cewa ta taba jin labarin cutar amma ba ta san illar cutar ba, inda ta kara da cewa, “Don haka a nawa bangaren, ina yin duk abin da ya dace don kare rayuwata. Sai dai yanayin da bandakunanmu suke ciki na da matukar hadari ga lafiyar mu.
Game da iyaye.
Wata mahaifiya mai suna Hafsat Shu’aibu, ta koka kan wannan lamarin da aka samu, inda ta ce hakki ne da ya rataya a wuyan makarantu su tabbatar da cewa ‘ya’yansu suna cikin koshin lafiya , a matsayinsu na iyaye, ta ce suna yin iya kokarinsu a gida don kare ’ya’yansu.
“Mu a matsayinmu na iyaye a gida muna yin iya ƙoƙarinmu. Amma duk wannan kokarin zai zama a banza tunda babu tsaftataccen ruwa da bandaki ga ya’yanmu a makarantunsu.”
Sai dai wani malami a Kawaji da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce nauyin ya yi yawa ga makarantun saboda matsalar kudi, shi yasa basa Iya yin abun da ya dace don kula da lafiyar dalibansu.
“Hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta samar wa makarantu duk wadannan na’urorin tsaftar da kuke magana akai. Kuma galibin bandakunanmu ba su da tsafta saboda rashin ruwa.
Da aka tuntubi yadda cutar ta ke, Dakta Aminu Auwalu Bala, likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya ce irin wannan cuta tana yaduwa kuma cikin sauki tana shafar mutane musamman yara.
Mutane su tabbatar sun wanke hannayensu kafin abinci da kuma bayan sun ci abinci. Su kuma yara, iyaye su samar musu da tsaftataccen ruwan sha a lokacin da za su je makaranta, su kuma malamai su rika fadakar da su kan yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar.”
Ya kara da cewa hakki ne da ya rataya a wuyan malamai su tabbatar masu sayar da abinci a makarantunsu suna samar da abinci mai tsafta kamar yadda ya kamata .
Gwamnati na yin iya kokarinta – Ma’aikatar Lafiya
SolaceBase ta tuntubi kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran, amma ya ce ba zai iya magana kan batun ba saboda ya yi tafiya zuwa Legas.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano na yin iyakacin kokarinta wajen daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar kwalara.
Da aka tambaye shi kan kokarin da ake yi a makarantun gwamnati, Abdullahi ya ce bai da masaniya kan wani yunkurin gwamnati a halin yanzu.
“Bayan haka, babu cutar kwalara a jihar Kano. Kuma game da ƙoƙarin da muke yi na rigakafin cutar a makarantu, ba zan iya cewa komai ba a zahiri saboda ba ni da masaniya. Amma zan bincika.”