Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jiha daga Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Akwai yiwuwar samar da sabuwar jiha nan ba da jimawa, sakamakon yadda aka gabatar da kudirin kafa jihar Tiga daga Kano a majalisar dattawan Najeriya.

Kudurin dokar wanda Sanatan Kano ta kudu Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar, wanda akan yi masa karatu na farko a ranar 10 ga Yuli, 2024.

Hajjin bana: An kammala jigilar dawo da Alhazan jihar kano gida

Kudirin doka mai taken “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Creation of Tiga State Bill, 2024 (SB.523)” na da nufin raba jihar Kano zuwa jihohi biyu, inda Tiga za ta zama sabuwar jihar da za a kirkireta daga jihar kano .

Talla

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Majalisar Dattawa ta karbi kudirin kafa Jihar Anioma a yankin Kudu maso Gabas, wanda Sanata Ned Nwoko daga Delta ta Arewa ya gabatar.

Abubunwan da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi

Bugu da kari, an gabatar da kudirin dokar kafa jihar Orlu, wanda Sanata Osita Izunaso da mai wakiltar Ikenga Ugochineyere, da kuma jihar Etiti suka gabatar, wanda dan majalisa Amobi Godwin Ogah da wasu ‘yan majalisa hudu daga al’ummomin da abin ya shafa suka dauki nauyinsa.

Akwai kuma kiraye-kirayen a kirkiro sabbin jihohi daga Legas da sauran sassan kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...