Daga Sani Danbala Gwarzo
Da asubahin wannan rana ta laraba ne jirgin karshe dauke da Jirgin dauke da alhazan jihar kano ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake kano.
Jirgin ya yi taso daga birnin Jeddah na kasar Saudiyya da misalin karfe 12:06 na safe, wanda hakan ke nuna an kammala dawo da alhazan jihar gida bayan kammala aikin hajjin bana.
Jirgin kamfanin Max Air da ya sauka a filin jirgin Mallam Aminu Kano da karfe 4:36 na safe, ya sauke alhazai 404 wadanda suka hada da jami’an gwamnati da mahajjata daga kananan hukumomi uku na kano:
1. Garun-Malam
2. Bebeji
3. Doguwa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar alhazai ta kasa NAHCON, sun tabbatar da gudanar da aikin dawo da su cikin kwanciyar hankali.
Abubunwan da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
Sanarwa da jami’an hulda da jama’a na hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano Sulaiman Abdullahi Daderi ya aikowa kadaura24, yace Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana godiyarsa ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da mahukuntan Saudiyya, da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Saudiyya, da kamfanonin jiragen sama da abin ya shafa, bisa goyon baya da hadin kai da suka ba su a lokacin gudanar da aikin hajji. .
Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya ce, “Mun ji dadin yadda dukkan alhazan mu suka gudanar da aikin Hajjinsu cikin nasara, kuma yanzu haka sun dawo gida lafiya, mun yaba da kokarin duk bangarorin da abin ya shafa wajen samun wannan nasara.