Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa namijin kokarin da yake yi na magance matsalolin ƴan fansho a jihar da kuma kula da ilimin ‘ya’ya mata.
Sani Abba Yola, Darakta a Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano, ya ce Sarkin ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya karbi bakuncin Kwamishinan Yada Labarai, Baba Halilu Dantiye da takwaransa na Kimiyya da Fasaha da Ƙere-ƙere, Alhaji Mohammed Tajo Othman a fadar Sarkin.
A cewarsa, Sarki Sanusi ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta mai da hankali ga ƴan fansho da a baya aka jefa su cikin halin ƙaƙanikayi saboda rashin biyan su haƙƙoƙinsu.
Ya kuma jaddada cewa, “Bambancin kula da rashin kula, wani lokacin kamar bambancin rayuwa da mutuwa ne ga mai karbar fansho ko iyalansa, wasu daga cikinsu sun mutu, mu tuna cewa dukkanmu muna da alhakin Allah Ta’ala kan hakkin cika wajibcinmu ga wadanda suka yi wa jihar hidima tsawon shekaru 35.”
Sarkin ya yabawa Gwamna Yusuf bisa kashe naira biliyan shida wajen biyan kudin fansho da aka yi a baya-bayan nan ga ‘yan fansho da kuma karin sakin naira biliyan biyar da aka ware domin ci gaba da biyansu, lamarin da ya rage wa ma’aikatan da suka yi ritaya raɗaɗi.
“Biyan Naira biliyan 11 a cikin shekara daya hakika abin yabawa ne,” in ji Sarki Sanusi.