Gwamnatin Kano za ta gina dakunan karatu a kananan hukumomi 44

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyar ta na samar da ingantattun dakunan karatu ga jama’a a fadin kananan hukumomin jihar 44 .

Mukaddashin sakataren hukumar kula da dakin karatu ta jihar Kano, Malam Suleiman Hodi Adamu ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa.

Ya ce makasudin aikin shi ne farfado da dabi’ar karatu da bincike a tsakanin dalibai da masu bincike da nufin inganta tsarin koyo mai inganci.

Kotu Ta Rushe Kwamitin da Gwamnan Abba Kabir ya Kafa Don Bincikar Ganduje

Malam Adamu ya kara da cewa hukumar ta ziyarci karatu na kananan hukumomi 23, cikin 44 dake jihar.

A cewarsa, rangadin wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na farfado da dakunan karatu da ake da su da kuma amfani da su domin ci gaban ilimi a jihar.

Talla

 

Mukaddashin sakataren zartarwa ya ce a karshen rangadin hukumar za ta mika rahoton ga ma’aikatar ilimi da nufin yin gyaran fuska kan yuwuwar samar da dakunan karatu a daukacin kananan hukumomi 44 na jihar.

“Gwamnatin Kano ta tallafa wa hukumarmu ta gudanar da rangadin duba dakunan karatu da muke da su a kananan hukumomi 23.

Rikicin Masarautar Kano: Alkali Ya Hana Lauyoyin Magana da Jaridu

“Mun je wurin ne da nufin farfado da su da kuma amfani da su, hakika wannan aikin zai farfado da dabi’ar karatu a tsakanin dalibanmu.

“Hakanan zai taimaka wa masu binciken mu wajen gudanar da bincike, sannan matasanmu za su koyi bincike.

“Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf a shirye take ta tallafa wa duk wani shiri da kuma ci gaban ilimi a jihar,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...

Kamata ya yi wajen Mauludi ya Zama waje Mai nutsuwa saboda ana ambaton Allah da Manzonsa – Mal Ibrahim Khalil

Shugaban Majalisar shuhurar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam...

Ra’ayi:‎Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello

‎ ‎Ra’ayi ‎ ‎Daga Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi), Jigo a Kwankwasiyya...