Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar dokokin jihar Kano ta musanta labarin da ake yadawa dake cewa ta ki dawo aiki ne saboda tsoron matsalar tsaro da ka iya tasowa saboda rikicin masarautar kano da ke ci gaba da faruwa a jihar.
Kakakin Shugaban Majalisar, Kamaluddeen Shawai ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya hakan a ranar Laraba, Inda ya ce “labarin bashi da tushe ballantana makama”.
Masu Garkuwa da Mahaifiyar Rarara sun Bayyana Abun da Suke Bukata Kafin su Sake ta
Shawai ya bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da duk wani rahoton da ke nuni da cewa majalisar ki dawo wa aiki ne saboda rashin tsaro da rikicin masarautar ya haifar.
“Batun Jin tsoron ko kai hare-hare ga majalisar ba komai ba ne illa shafin gizo da wasu marasa kishin kano suke yadawa.
“Majalisar za ta dawo zamanta nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Ya nanata kudurin majalisar na yin aiki tare da Gwamna Abba Kabir-Yusuf domin ci gaban jihar baki daya.
Shawai ya bukaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba da addu’ar samun zaman lafiya da hadin kai a jihar da kasa baki daya.(NAN)