Daga Wasila Ladan
Kungiyar Matan Sojojin ruwa ta Nigeria (NOWA) ta bayyana baiwa mata tallafi domin su dogara da kawunan su, a matsayin hanyar gini al’umma da magance talauci a tsakanin al’umma.
Mataimakiyar shugabar kungiyar ta kasa Zainab Akpan ce ta bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja.
“Tallafawa mata yana da mahimmanci kuma zai taimaka wajen magance rikicin jinsi a cikin gidaje da kuma cikin al’umma. A halin da ake ciki a yau, tallafawa mata yana magance ƙalubalen talauci, rikicin jinsi a gidajensu da wuraren aiki, da ma cikin al’umma”. Zainab Akpan
Da dumi-dumi: Masu Tapswap sun daga ranar da zai fashe
Mrs Akpan ta ce tallafawa mata yana ba su damar ba da gudummawa sosai ga iyalansu, tattalin arzikin kasa, da kuma kara musu kima a idon duniya baki daya .

Ta kuma bayyana cewa tallafawa mata ya shafi muhimman abubuwa guda biyar na ci gaban mata: zamantakewa, tunani, ilimi, tattalin arziki da siyasa.
Zainab Akpan ta ce tallafawa mata na nufin karfafa al’umma, gina al’umma, samar da muhimmiyar alaƙa tsakanin matasa da maza a gida da kuma cikin al’umma, suna tasiri ga al’ummominsu.
Wakiliyar gidan rediyon Najeriya kuma sakatariyar kungiyar NAWOJ ta kasa Wasilah Ladan ta ruwaito Mrs Akpan ta ce tallafawa mata na basu kwarin gwiwar hidimtawa al’umma kamar yadda wasu mata suka yi tasiri sosai a cikin al’umma, matan da za a iya kafa misali da su a irin wannan fage su ne kamar su: Ladi Kwali, Amina J. Muhammed, Malala Yousafzai, Hajiya Fatima Kurfi, Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma Dora Akunyili.