SMEs : Sama Da Kashi 70 Na Mambobinmu Sun Sami Tallafin Dubu Hamsin Hamsin – Nassi.

Date:

Daga Bashir Gasau.

Ƙungiyar masu ƙanana da matsaƙaitan Masana’antu ta Najeriya ta yabawa Gwamnatin Nigeria ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, a bisa yadda sama da kashi 70 na mambobin ƙungiyar suka sami tallafin Naira dubu hamsin- Hamsin ta ƙarƙashin shirin tallafawa masu ƙananan Sana’oi wato (Nano Project).

Ma’ajin ƙungiyar na Najeriya Dakta Abubakar Tanko Bala ne ya yi yabon a madadin Shugaban ƙungiyar Chief Dakta Solomon Daniel Vongfa, ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA a yau Asabar, inda ya ce suna yaba wa Gwamnatin ne musamman Ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari Dakta Doris Nkiruka Uzoka duba da ta ɓangarenta ne suka sami wannan dama.

Yadda Al’umma ke Kallon Yan Fim Abun na Damu na -Jarumi Amal Umar

Dakta Bala ya ƙara da cewa, Waɗannan muhimman shirye-shirye za su bayar da tallafin da ake bukata ga ƙanana da matsaƙaitan masana’antu a faɗin Najeriya, ta yadda mutane da yawa zasu sami alfanu ta fuskoki da dama kamar bunƙasa kasuwancin su, samar da ayyukan yi, dama haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasa.

Haka kuma ƙungiyar ta yi fatan samun cikakken haɗin kai da goyon bayan ma’aikatar kasuwanci da zuba jari a sauran shirye-shiryen, domin aiwatar da su cikin nasara da kuma ƙara girman tasirin su ga mambobin NASSI da SMEs dake faɗin ƙasar.

Mafi ƙarancin albashi: NLC ta Mayarwa da Gwamnonin Nigeria Martani

A ƙarshe ƙungiyar ta jaddada godiyar ta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari Dakta Doris Nkiruka Uzoka, harma tayi fatan mambobin ƙungiyar dama sauran al’ummar ƙasar zasu yi amfani da tallafin ta hanyar da ta dace.

Wannan shiri dai na ƙarƙashin Manyan tsare-tsaren Gwamnatin Bola Tinubu na sabunta fatan alheri, ta yadda ake bada tallafin domin inganta rayuwar ‘yan ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...