Turkiyya ta bayyana dalilan da suka sa ta koro ƴan Nijeriya 103 zuwa gida

Date:

Gwamnatin tarayya ta karbi ƴan Najeriya kimanin 103 da aka koro daga kasar Turkiyya bisa wasu dalilai da suka shafi bakin haure da suka hada da ƙarewar wa’adin biza da shiga ƙasar ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu.

Alhaji Tijani Ahmed, kwamishinan hukumar kula da ƴan gudun hijira da bakin haure ta kasa (NCFRMI) ne ya bayyana haka a yammacin jiya Juma’a, a lokacin da ake tantance waɗanda aka koro din a Abuja.

Mafi ƙarancin albashi: NLC ta Mayarwa da Gwamnonin Nigeria Martani

Ahmed, wanda Amb. Catherine Udida, darakta mai kula da al’amuran hijira a hukumar ya wakilta, ya ce hukumar ta yi tsammanin za a aiko mutane 110 amma sai ta karbi 103, dukkansu maza.

“Wasu daga cikinsu sun shafe wasu watanni a sansanin waɗanda aka koro, kuma yanzu da suke nan, muna fatan za mu bi diddigin duk wasu zarge-zargen da aka rubuta a kundin bayanansu.

Asibitin Best Choice Ya Fara Kula da Masu Lalurar Mafitsara

“Za mu bi ta fom din tantancewa, saboda wasu sun ce an kwace fasfo dinsu.

“Za mu bi diddigin hukumomin Turkiyya, saboda har yanzu fasfo mallakin Tarayyar Najeriya ne,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...