Mafi ƙarancin albashi: NLC ta Mayarwa da Gwamnonin Nigeria Martani

Date:

Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, ta mayarwa da wasu gwamnomin jihohin ƙasar martani kan ƙoƙarin da suke na ganin an bai wa kowacce jiha damar yanke abin da za ta iya biya a matsayin mafi ƙarancin albashi, saɓanin ƙokarin da ake yi na ganin an amince da farashi na bai ɗaya.

Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewar da alama gwamnonin ba su fahimci tsari da dokar albashi mafi ƙanƙancin ba.

Kwamared Benjamin Anthony, mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewar albashi mafi ƙanƙanata ake son a biya, wanda kuma a duniya ma idan aka kayyade albashin mafi ƙaranci da za a biya, babu wani sashe ko jiha da za ta biya ƙasa da yadda aka ƙayade, tunda doka ce ta bai ɗaya, wadda ita kanta ƙungiyar ƙwadago ta duniya ta amince da ita.

Gwamnatin Kano ta yi tsokaci kan tutar da aka sanya a fadar sarki Aminu Ado Bayero

Kwamared Benjamin Anthony, ya kara da cewar “rashin adalci ne da ake fama da shi a kasar, a ce ga gaskiyar abin da tattalin arziki ke cewa, a ce ga albashi mafi karanci da za a biya, amma a ce ba za a bi ba, ko da gwamnati ta ce zata bayar da naira dubu sittin da biyu (N62, 000) mun yi tambayar nawa ne kudin mai a ciki ?, nawa ne kudin mota nawa ne kudin makaranatar yara?, nawa ne kudin haya? inji shi.

Ya Kuma ja hankalin gwamnomi da ita kanta gwamnatin Najeriya da cewar akwai bukatar su duba halin da yan kasar ke ciki, da ya sa suka bukaci mafi karancin albashi na naira dubu ɗari biyu da hamsin, wanda suka ce a hakan ma ba lallai ta biya buƙatar da ake so ba.

“ Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, sun ce za su biya dubu stittin da biyu, mu kuma mun ce sai dubu dari Biyu da hamsin, idan ka lura yanzu nawa ne kudin buhun shinkafa? Ya kai wajen Naira dubu Taminin to kaga kenan albashin da ake cewa za a biya mafi karanci ba ma zai iya saya wa ma’aikaci ko rabin bushun shinkafa ba.

Yanzu haka dai magana na hannun shugaban ƙasar Najeriyar Bola Ahmed Tinubu, don haka kungiyar ta ce tana jiran ta ga matakin da zai ɗauka, wanda daga nan za su fitar da tasu mastayar.

El-Rufa’i ya yi riga Malam Masallaci – Majalisar dokokin Kaduna

Maratanin ƙungiyar ƙwadagon ta Najeriyar na zuwa ne, bayan da wasu daga cikin gwamnonin jihohin ƙasar ke cewar ba za su iya biyan ko da Naira dubu 60 ko dubu 62 da gwamantin ƙasar ta yi wa ƴan ƙwadagon tayi ba a msatyin albashi mafi karanci.

Sai dai wasu daga cikin gwamnonin ƙasar irin su na Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar Gwamna Nasiru Idris Ƙauran Gwandu ya ce a shirye yake da ya biya ko nawa aka aminceda shi a mastayin mafi ƙarancin albashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...