Daga Rahama Umar Kwaru
Shahararren asibitin nan na da ya jima yana kula da lafiyar al’umma mai suna Best Choice Specialist Hospital ya nanata kudurinsa na samar da ingantaccen aikin kula da lafiya ta hanyar samar da kwararru da kayan aiki na zamani don ceton rayukan al’umma.
Shugaban asibitin kwararru na Best Choice, Auwal Lawal Muhammad ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da manema labarai a Kano.
Auwal Lawal ya jaddada cewa asibitin na cike da kayan more rayuwa na zamani da na’urorin kiwon lafiya na zamani. Ya ce suna da tarin kwararrun likitocin mafitsara wato urologist wadanda suka shirya tsaf don magance duk wata lalura ta mafitsara kowacce irin ce.
A cewarsa, asibitin ya fadada ayyukansa na kiwon lafiya ta hanyar yin aiki akan duk nau’in wata cuta da ta shafi mafitsara da dai sauransu.
El-Rufa’i ya yi riga Malam Masallaci – Majalisar dokokin Kaduna
Da yake asibitin Best Choice yana da rijista ya tanadi ƙwararrun likitocin mafitsara wadanda suke da gogewa mai tarin yawa, da kayan aiki na zamani don kula da lafiyar majiyata.
Bugu da ƙari, hukumar gudanarwar asibitin ta na baiwa marasa lafiya tabbacin basu kulawa ta musamman da samar musu da walwala ba tare da wata matsala ba.
A cewar Lawal, idan marasa lafiya suka ziyarci asibitin suna samun lafiya, wannan kuma yana da alaka da kwarewa da kyakykyawan tsarin da asibitin ke da shi wajen kula da masu lalurar mafitsara.
Ya bukaci marasa lafiya musamman masu fama da toshewar mafitsara da sauran cututtukan mafitsara wanda ya hana su gudanar da al’amuran su na yau da kullum da su garzayo domin duba lafiyarsu.
Shugaban ya kara da cewa asibitin BEST CHOICE SPECIALIST ya koma wurinsa na dindindin da ke kusa da Tal’udu Roundabout, daura da Kwalejin Shekh Bashir El-rayya, Aminu Kano Way, Kano, inda hedkwatarsa ta ke a yanzu. Kuma Asibitin ba shi da alaƙa da kowane asibiti da ke tsohon wurin da ya taso ba.
Baya ga shahara a aikin mafitsara, Lawal ya shaidawa manema labarai cewa asibitin Best Choice yana kula da masu fama da jinyoyi da dama, waɗannan da suka haɗa da duk nau’in tiyata kowace iri, sannan muna da likitocin yara, likitan masu lalurar hankali, likitan hakori, fata, kashi, likitan mata da dai sauransu.
Kuma muna da dakin gwaje-gwaje, kantin magani, da sashin kula da jarirai na zamani da dai sauransu.