Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Da sanyin safiyar wannan rana ta alhamis an wayi gani da ganin tuta a samar gidan sarki na Nasarawa Inda mai martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero yake zaune.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an fara dambarwar masarautar Kano tun lokacin da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya ce ya dawo da Sarki Sanusi II man karagar mulkin Kano.
Tun ranar litinin a kafafen sada zumunta ake ta yada cewa za a saka tutar Shehu Usman Danfodio a gidan sarkin dake Nasarawa a birnin kano.
Tsige Sarkin Musulmi: Gwamnatin Sokoto ta Mayarwa Kashim Shettima Martani
To Amma ba a saka tutar ba sai da safiyar wannan rana ta alhamis 27 ga watan yuni 2024.
Masana dai sun ce akan sanya tuta a duk gidajen Sarakunan da Shehu Usman Danfodio ya basu tutar Addinin Musulunci.
Ita kuma tutar tana nuna alama ce na cewa sarki yana gari ko baya gari.
Karin Haske Kan Hukuncin Kotu Game da Rikicin Sarautar Kano
Tuni dai wata majiya a gidan sarkin ta tabbatar wa da kadaura24 cewa tuni Sarki Aminu Ado Bayero ya nada sabon sarkin tuta, wanda aikin sa shi ne ya rika kula da tutar idan sarkin yana nan ko idan baya gari.
Wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki kadan da gwamnatin jihar kano ta ware kusan Naira miliyan 100 domin gudanar da gyare-gyare a gidan sarkin dake Nasarawa, bayan tari ikirarin rushe katangar gidan.