El-Rufa’i ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna a Kotu

Date:

 

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shigar da ƙara a gaban kotu, inda yake ƙalubalantar majalisar dokokin jihar kan zarge-zargen da ta yi masa na almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.

Gwamnan ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a wata babbar kotun tarayya da ke birnin Kaduna.

Wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labaru, Muyiwa Adekeye, ta ce Elrufa’i ya shigar da ƙarar ce domin tabbatar da haƙoƙoƙin da yake da shi na kare kai game da binciken da majalisar dokokin jihar ta ce ta yi a kansa.

Lauyan El-Rufa’i, AU Mustapha ya ce tsohon gwamnan ya ɗauki matakin ne ganin cewa yana da hakkin a saurare shi a duk wani mataki na bincike ko kotu da za a ɗauka kansa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Tsige Sarkin Musulmi: Gwamnatin Sokoto ta Mayarwa Kashim Shettima Martani

Saboda haka El-Rufa’i ya buƙaci kotun ta ayya rahoton kwamitin majalisar dokokin jihar kan binciken ayyukan gwamnatinsa a matsayin haramtacce, wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma ya saɓa wa tanadin kundin tsarin mulki na jin ta-bakin wanda ake zargi.

Dama dai tsohon gwamnan ya yi watsi da rahoton kwamitin, inda ya bayyana shi a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.

Cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce ya bauta wa Kaduna “da gaskiya kuma yana alfahari da abubuwan da ya yi”.

“El-Rufai ya bi duk wasu dokoki a ayyukansa lokacin da yake gwamna…ya kamata a yi watsi da wannan binciken na ƙeta a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.”

A farkon watan Yuni ne wani kwamiti da majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa ya gabatar da rahotonsa.

 

Lokacin da ya gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa’i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa’ida wajen cin bashin ba.

 

Wasu daga cikin laifukan da rahoton ya ce ya bankaɗo game da gwamnatin El-Rufa’i su ne:

Tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayu 2023, shugaban ɓangaren zartarwa na jihar Kaduna ya karya ƙa’idojin aikin ofishinsa kamar yadda suke a kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska.

Jefa jihar cikin ƙangin bashi na cikin gida da waje ta hanyar ha’inci ba tare da dalili ba, waɗanda suka zarce jimillar ɗaukacin basukan da jihar Kaduna ta taɓa ci daga shekarar 1965 zuwa 1999, kuma yawanci an karɓo bashin ne ba tare da bin ƙa’ida ba.

Bayar da kwangiloli barkatai ba tare da bin ƙa’ida ba kuma ba tare da bin diddigin aiwatarwa ba, wanda hakan ya haifar da yin watsi da kwangiloli da dama duk kuwa da kuɗaɗen da aka biya.

Bayar da izinin cire maƙudadan kuɗaɗen naira da dalar Amurka ba tare da bayanin yadda aka yi amfani da su ba, wanda hakan ya hana jihar samun isassun kuɗaɗen da za ta aiwatar da ayyukan ci gaba.

Haɗa baki da kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnati domin ha’intar gwamnati ta hanyar umurtar hukumar KADPPA ta biya ƴan kwangila kuɗi ba tare da bin ƙa’ida ba, kamar yadda yake ƙunshe a wata wasiƙa mai kwanan wata 21st Yuni, 2021.

Karkatar da kuɗi da halasta kuɗaɗen haram wanda ya saɓa da dokoki da ƙa’idoji, kuma ya kamata a miƙa shi ga hukumomin tsaro domin gudanar da zuzzurfan bincike tare da ɗaukar matakan da suka kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...