Daga Rukayya Abdullahi Maida
Mai magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya zargi rundunar ‘yan Sanda ta kasa reshen jihar da daukar bangaranci a Dambarwar Masarautar dake faruwa a jihar.
Idan za’a iya tunawa tun bayan da majalisar dokokin jihar kano ta rushe dokar da ta samar da karin masarauta 4 a jihar tare da dawo da Sarki Sanusi II a matsayin Sarkin Kano Ake ta dambarwa kan batun.
Hakan tasa sarki Aminu Ado Bayero ta dawo Kano, gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinan ‘yan sandan daya fidda sarki Aminu Ado bayero daga fadar sarkin ta gidan Rumfa.
Mai Kula da Mukullin Ka’aba Al-Shaiba ya Rasu
Sanusi Bature wanda shi ne daraktan yada labaran Gwamnan jihar Kano ya bayyana hakan ta cikin wata hira da tashar Talabijin ta Arise a ranar Juma’a.
Ya ce a matsayin gwamnan Kano na wanda kare rayuka da dukiyoyin al’umma ya rataya a wuyansa, Amma ya baiwa kwamishinan yan sandan jihar umarni har sau biyu yana bijirewa umarnin.
” Ba mu sani ba ko yan sanda za su mutunta umarnin da gwamnan ya basu game da Fitar da Aminu Ado Bayero daga gidan Sarki na Nasarawa domin yan sanda sun sauki bangaren a wannan dambarwa, basa karbar umarni daga gwamnan”. Inji Sanusi Bature
Ya ce bai dace yan sanda su rika bijirewa umarnin gwamna ba a matsayinsa na shugaban tsaro a jihar, ya kamata su bashi hadin kai ya sauke nauyin da kundin tsarin mulkin Nigeria ya ba shi.
Idan za a Iya tunawa kadaura24 ta rundunar ‘yan sandan bisa jagoranci CP Usaini Gumel tayi fatali da umarnin gwamnan na fitar da sarki Aminu Ado Bayero daga gidan sarki na Nassarawa, inda yace ba zasu bi umarnin ba saboda batun yana gaban kotu.
Ta cikin ganawar Sunusi Bature ya bayyana cewa hukuncin Kotun tarayya su ya bawa nasara domin kuwa kotun bata rushe dokar data sauke tsoffin sarakunan jihar guda biyar ba.