Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta ce dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram, amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya ce ba dai-dai bane gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunkuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.
Mai shari’a Liman ya ce “A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi”.
Ya kamata Gwamnatin Kano ta Mutunta Umarnin Kotu – Dr. JY
Kotun ta ce “An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari’ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba.
”Alkalin ya ce tun da har gwamna da kansa ya ce ya samu labarin umurnin kotu, to ya saɓawa doka da ya yi gaban kansa wajen aiwatar da sabuwar dokar masarautun jihar Kano.
“Waɗanda ke kare kansu a shari’ar na sane da umurnin kotun duk da cewa ba a aika musu da kofin umurnin ba. Amma sun gani a kafafen soshiyal midiya, a don haka ba daidai bane su kawar da kai”, in ji Alkali Liman.
Mai shari’a Liman ya mayar da wannan ƙara zuwa wata kotun tarayyar karkashin mai shari’a Amobeda Simon amma har sai an kammala sauraren karar da ɓangaren gwamnati suka ɗaukaka.
Wannan al’amari na dambarwar masarautar Kano, tana ci gaba da ɗaukar hankali inda jama’a ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.
A watan Mayun da ya gabata ne dai ‘yan majalisar dokokin jihar ta Kano suka yi ƙudirin dokar inda kuma ba tare da ɓata lokaci ba gwamnan Kano Abba kabiru Yusuf ya sanya mata hannu ta zama doka.
Bisa dokar ne gwamnan ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe shi a 2020.
To sai dai kuma a ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi mai sarautar Sarkin Dawaki Babba ya ƙalubalanci dokar a babbar kotun tarayyar da ke Kano, inda ya nemi alƙalin da ya rushe dokar a matsayin haramtacciya.
Yanzu-yanzu: Kotu ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Sarautar Kano
‘Kowa na kan bakarsa’
Kimanin wata guda kenan dai ana zaman tankiya tsakanin Alhaji Aminu Ado Bayero wanda tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa a matsayin Sarkin Kano na 15 a 2020, bayan tsige Muhammadu Sanusi II wanda yanzu gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da shi a matsayin Sarkin Kano na 16 bayan tunɓuke Alhaji Aminu Ado Bayero.
Tun dai wannan lokaci ne mutanen biyu ke ikirarin halascin sarautar Kano inda suke gudanar da al’amuran sarauta daga gidaje biyu.
Yayin da Muhammad Sanusi ke harkokin sarauta daga gidan Dabo, shi kuwa Aminu Ado na yin nasa harkokin ne daga gidan Sarki na Nassarawa.
Gargaɗin rundunar ƴansanda
Rundunar ƴansanda ta jihar Kano a wata sanar da ta fitar ta gargaɗi al’ummar jihar da su guji abubuwan da ta ce ka iya janyo tarzoma kamar haka:
Za ta ci gaba da sanya ido kan haramcin duk wani nau’in zanga-zanga ko jerin gwano ko taron jama’a da ya saɓa ƙa’ida. Kuma za ta ɗauki mataki a kan duk wanda aka kama da aiwatar da hakan ko kuma kitsa yin hakan
An baza dakarun tsaro a wurare muhimmai a birnin Kano.
An gargaɗi duk wasu ’yan ƙungiyar sintiri da ƴan daba da su janye jikinsu daga bai wa kowane irin mutum kariya maimakon jami’an tsaro.