Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Kano Ta Ba da Tabbacin Inganta Jindadin Ma’aikata

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta inganta walwala da kuma yanayin aiki ga ma’aikata a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha Kano.

Gwamnan wanda mataimakinsa Alhaji Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an biya ma’aikatan da suka yi ritaya hakkokin su a kan lokaci da kuma kudaden fansho domin inganta rayuwarsu.

Ya kuma yi nuni da cewa, ana shirin kaddamar da tsarin da ya dace na samar da gidaje ga ma’aikata, yana mai jaddada cewa idan aka kaddamar da shirin zai bai wa ma’aikata damar mallakar gidaje a farashi mai rahusa.

Kungiyar Kwadago ta yi fatali da karin albashin da Tinubu ya yiwa ma’aikatan Nigeria

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen bunkasa ilimi, noma, da samar da lafiya da dai sauransu.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan jihar Kano da su sakawa gwamnatin ta hanyar jajircewa da sadaukarwa a wajen aiyukan su.

Tinubu ya karawa ma’aikatan Nigeria albashi

A nasa jawabin, shugaban kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa ya taya gwamna Yusuf murnar samun nasara a shari’ar da aka yi a kotu.

Ya zayyana wasu daga cikin nasarorin da Gwamna Yusuf ya samu karkashin gwamnatin sa kamar

biyan albashi a kan lokaci, cikakken biyan fansho ba tare da yanke musu komai ba, dawo da biyan albashi ga Ma’aikatan da gwamnatin da ta gabata ta dauka aiki bayan zaben 2023.

Sauran sun hada da biyan hakkokin wadanda suka yi ritaya da na wadanda suka mutu da daukar nauyin ma’aikata zuwa jami’o’in kasashen waje domin neman ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...