Gwamnatin Legas za ta fara ciyar da mutane dafaffen abinci kyauta

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Gwamnatin Legas za ta fara ciyar da mutane dafaffen abinci kyauta
Gwamnatin Legas za ta fara ciyar da mutane dafaffen abinci kyauta
Mai bai wa Gwamna Sanwo-Olu shawara kan watsa labarai Jubril A Gawat ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na X a ranar Alhamis.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da yin haihuwa kyauta, ciki har da tiyata a asibitocin gwamnati da ma ba da wasu magungunan duka kyauta.

Gwamnatin Jihar Legas da ke Kudancin Nijeriya ta sanar da cewa za ta fara raba wa mutane dafaffen abinci kyauta sau ɗaya a kowace rana.

Zanga-zanga: Kungiyar Kwadago ta yiwa Hukumar DSS Martani

Mai bai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shawara kan watsa labarai Jubril A Gawat ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na X a ranar Alhamis.

Ya ce gwamnatin za ta yi wannan aiki ne ta hanyar neman masu abincin sayarwa da za su dinga dafa abincin mutum 1,000 a kowace ƙaramar hukuma.

Wannan mataki na gwamnatin na zuwa ne a lokacin da al’ummar Nijeriya ke kokawa kan matsalar ƙarancin abinci saboda tsadarsa sakamakon hauhawar farashi.

Mau sharhi na danganta hauhawar farashin da tashin da dala ke yi, inda darakar naira kuma ke yin ƙasa a kusan kowace rana.

Yadda kamfanonin Kirifto ta Haddasa Tashin Farashin Dala a Nigeria

Baya ga matakin ciyar da jama’a dafaffen abinci da gwamnatin Jihar Legas ta sanar, ta kuma ce daga yanzu ta mayar da haihuwa a asibitocin gwamnatin kyauta.

“Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da yin haihuwa kyauta, ciki har da tiyata a asibitocin gwamnati da ma ba da wasu magungunan duka kyauta,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hasashe 6 da Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kuma suka tabbata a siyasar Kano

‎ ‎ ‎ ‎Musa Iliyasu Kwankwaso na daga cikin fitattun ’yan siyasar...

Hukumar Hisbah Za ta Tura Sama da Jami’ai 1,000 Don Samar da Tsaro a Ranar Takutaha a Kano

Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano...

Kotun tafi-da-gidanka ta KAROTA ta ayyana neman wani direba ruwa a jallo

Alkalin Kotun Majistare da ke gudanar da shari’ar masu...

Muna rokon gwamnatin Kano ta haramta daukar fasinjoji a bakin titi – Kungiyar Direbobin Haya

Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta ƙasa reshen Kano dake...