NAHCON ta Bayyana Yadda Saudiyya Ta Rage Kudin Aikin Hajjin Bana

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hukumomi a kasar Saudiyya sun yi ragin kudin Hajji ga maniyyatan da za su sauke farali a bana, 2024.

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar cewa shugabata, Jalal Ahmad Arabi, ne ya nemo ragin da aka yi, Wanda ya shafin kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake wa alhazai a Saudiyya.

Mai magana da yawun hukumar NACHON, Fatima Sanda Usara ce ta sanar da hakan a ranar Laraba, inda ta ce a sakamakon haka, Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kudin tikitin jirgin da aka biya a 2023, masauki a Madina daga Riyal daga 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.

Yan Kasuwar Canji na Abuja sun sanya ranar rufe Kasuwar

“Zama a Muna da Arafa da Muzdalifa kuma an rage shi zuwa Riyal 5,393 zuwa 4,770,” in ji ta.

Sai dai duk da haka, sanarwar ba ta bayyana ko NAHCON za ta yi wa maniyyayatan Najeriya ragin kudin kujera daga Naira miliyan 4.5 da ta sanar tun da farko ba.

Wutar Lantarki Ta Kashe Barawon Taransufoma

Kazalika ana hasashen duk da saukin da wannan saukin da Saudiyya ta yi, da wuya maniyyayatan Najeriya su shaida sauƙin — daga Naira miliyan 3 da suka biya a 2023 — sakamakon tashin farashin Dala.

Farashin kudaden kasashen waje musamman Dala sai kara karuwa yake a Najeriya, lamarin da ke kara haifar da tsadar rayuwa a kasar.

Akasari ana biyan kudin aikin Hajji da sauran huldodin kasa da kasa, kamar aikin Hajji da sauransu ne da Dala ko sauran kudaden kasashen waje.

Faduwar darajar kudin Najeriya, Naira da tashin dala da danginsa a kasar ta sa a duk shekara kudin aikin Hajji karuwa.

A sakamakon haka ne aka samu karin kashi 50 a kudin aikin Hajjin 2024 a kan na 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu taguwar maniyyayatan Najeriya da za su sauke farali a bana a sakamakon tsadar kudin kujera.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...