Kotu ta gindaya sharudda 2 kafin bada belin Danbilki Kwamanda

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Kotun majistiri dake Noma’s Land a jihar Kano ta bada belin Danbilki Kwamanda bayan da lauyan Roki Kotun.

“Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an kama Danbilki tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa Zarginsa da yin kalaman da zasu iya tunzura al’umma kan batun masarautun jihar kano”.

Yayin zaman ta na wannan rana kotun tace laifin da ake tuhumar Danbilki Kwamanda laifi ne da za’a iya bayar da shi beli don haka alƙalin kotun yace ya bayar da shi beli kan sharudda guda biyu.

Kotu a Kano ta dauki mataki kan hukumar Hisbah, bayan da wasu masu otel sukai karar ta

A zantawarsa da manema labarai bayan fitowa daga kotun lauyan Danbilki Kwamanda Barr. Ibrahim Chedi yace sharuddan belin da kotun ta gindaya sun:

1. Dole Danbilki Kwamanda ya Samu Mutane biyu da zasu tsaya masa, guda ya zama babban sakatare a gwamnatin jihar Kano sannan kuma dayan ya zama hakimi.

2. Kuma za’a ajiye kuɗi kimanin Naira Miliyan Daya.

NAHCON ta Bayyana Yadda Saudiyya Ta Rage Kudin Aikin Hajjin Bana

” Zan zamu fara kokarin Cika wadannan sharudda, amma idan mun ga bazamu iya cikawa ba, zamu nemi kotu ta sassauta mana sharuddan”. Inji Barr. Chedi

 

Kotun da dage zaman Shari’ar har sai ranar 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2024, kuma tuni an wuce da wanda ake tuhuma gidan gyaran hali kafin ya Cika sharuddan belin da aka gindaya masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...