Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Dangane da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kullum, ‘yan kasuwa sun koma yin salloli da addu’o’i domin neman taimakon Allah a jihar Kano.
Yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya zuwa watan Disambar 2023 ya kai kashi 28.92 cikin dari, kuma yana karuwa tsawon watanni 11 a jere.
Majiyar kadaura24 ta BizPoint ta rawaito yadda ‘yan Najeriya ke kara nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Kotu a Kano ta dauki mataki kan hukumar Hisbah, bayan da wasu masu otel sukai karar ta
A cikin wani faifan bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta a ranar Alhamis, an ga wasu gungun ‘yan kasuwa suna gudanar da salloli da addu’o’i na musamman a kasuwar Kantin Kwari da ke jihar Kano, babbar kasuwar sayar da kayan sawa a Najeriya da kuma yankin kudu da Sahara.
An yi imanin cewa an nadi bidiyon ne a ranar Laraba yayin da ‘yan kasuwar da abin ya shafa ke gudanar da salloli a titin Bayajidda da ke kasuwar Kantin Kwari a cikin birnin Kano.
A cikin dogon faifan 1:45, an ji muryar wani mutum, wanda ake kyautata zaton dan kasuwa ne a kasuwar, yana cewa sun ga dacewar fara salloli da addu’o’i na musamman ne domin neman taimakon Allah kan mawuyacin halin da ake ciki a kasuwar da kasa baki daya.
NAHCON ta Bayyana Yadda Saudiyya Ta Rage Kudin Aikin Hajjin Bana
Muryar ta koka kan yadda farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi a kasar, inda ta ce “yau mafi kankantar kuɗin atampa mai kyau shi ne N8,000 yayin da Atampar roba kuma ta kai N3,000.”
Mutumin da ke cikin faifan bidiyon ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su yi koyi da ‘yan kasuwar ta hanyar komawa ga Allah domin neman taimakonsa don kawo wa jama’a sauki.
“A yau mun yanke shawarar gudanar da wannan taro na musamman na salloli domin neman taimakon Allah a cikin wannan mawuyacin hali da muka tsinci kanmu a ciki.
“Shugabannin mu ba su yi mana adalci ba kuma Allah zai hukunta ku. Kun nemi kuri’un mu. Mun shafe lokacinmu, a cikin rana mai zafi don zaben ku kuma mun tabbatar da kuri’unmu a gare ku amma wannan shi ne sakamakon abun da zaku yi mana”.
“Shugabannin mu kullum suna alkawuran karya ba komai a kasa. Kuna fakewa da dalar Amurka don yaudarar ‘yan Najeriya.
“Ba shugabanni kadai ba, ’yan kasuwa ma na da laifi. Sun ba da gudummawa ga matsalolin da muke ciki. Mun da Allah kuma wallahi Allah sai yayi mana maganin ki ,” in ji mutumin.