Daga Rahama Umar Kwaru
Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa.
Kadaura24 ta rawaito mai shari’a John Okoro wanda ya karanta hukuncin a ranar Laraba, ya yi watsi da karar da ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aisha Dahiru ta shigar.
Yadda Aka Shawo Kan Likitocin Asibitin Murtala dake Kano Suka Koma Bakin Aiki
A yayin da ya yi watsi da karar da ta shigar bisa rashin cancantar ta, alƙalan biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro sun bayyana cewa, abin da Kwamishinan Zabe (REC), Hudu Ari ya aikata rashin gaskiya ne kuma ya aikata laifuka babba.
Sabon Gwamnan Kogi Ya Zo da Sabon Salo a Dimokaradiyyar Nigeria
Mai shari’a Okoro ya kara da cewa, jami’in tattara sakamakon zabe shi ne ya cancanta ya fadi sakamakon ba Ari ba.
Ya bayyana cewa dokar zabe ta dora alhakin bayyana sakamakon zabe akan wanda aka nada a matsayin jami’in tattara sakamakon zaben, kuma wannan jami’i shi ka dai ne ke da ita ba wani ba.